Bayan gaisuwa tare da fatan kana cikin Dausayin Rahamar Ubangiji, Allah Ya sa haka Amin.
A ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2021 kake cika shekaru 11 da amsa kiran Mahaliccinmu.
- Sun kashe dan makwabci bayan karbar kudin fansa
- Likitan da ya ba da gudunmawar kashe Osama ya nemi a sake shi
- An bankado ma’aikatan bogi 668 a Gombe
- Yadda ’yan Boko Haram suke farautar malamai a Geidam
Tabbas ’yan Najeriya mun yi rashin nagartaccen shugaba, adali, mai gaskiya da kokarin kamanta ta, masanin harkokin mulki da yin abin da ya kamata, kuma mai ilimi da hangen nesa.
A yayin da nake rubuto maka wannan wasika, idanuwa cike suke da hawaye masu zafi, zuciyata kuna na cike da radadin irin halin da kasar da kake kauna da son ganin ci gabanta, wadda ka yi kokarin dora ta a turba ta kwarai a lokacin rayuwarka, ta shiga, kasancewar a yanzu ta dauko hanyar wargajewa, abubuwa sun tabarbare.
Na rubuto maka wannan wasikar ce domin bayyana irin juyayi da halin zullumi da ’yan Najeriya musamman a yankin Arewa suka tsinci kansu bayan rasuwarka. Wannan ya faru ne sakamakon fatali da aka yi da kyawawan manufofinka.
Ko da yake na san wasikata ba za ta riske ka ba, amma ina da yakinin za ta kai ga iyali da masoyanka masu kishi da son cigaban kasar nan, wadanda suke maka addu’a a koyaushe —kuma tabbas addu’o’in za su riske ka da yardar Allah, domin ka nuna mana kauna, ka kuma so ci gabanmu. Shi ya sa zukatanmu ke ci gaba da begen ka har yanzu.
Kamar yadda ’yan Najeriya za su yi maka shaida a ranar gobe kiyama a kan yadda ka bijiro da kudurori bakwai (Seven Point Agenda), lokacin da ka hau kujerar shugabancin Najeriya, wadanda ka bullo da su da nufin kai kasar zuwa ga tudun mun-tsira.
Kudurorin su ne:
- Inganta wutar lantarki
- Wadatar da kasa da abinci
- Habaka arzikin kasa
- Bunkasa harkokin sufuri
- Garanbawul kan yadda ake mallakar filaye
- Samar da tsaro
- Inganta Ilimi
Sai dai kash! An yi watsi da kudurorin naka masu matukar alfanu bayan rasuwarka.
A yau an wayi gari yankin Arewacin Najeriya musamman mahaifarka da jiharka, wato Katsina da Kaduna sun zamo sansanin ’yan bindiga da ’yan fashin daji.
Rayuwa ta zama babu tabbas a wadannan jihohi, manoma sun kaurace wa gonakinsu, ’yan kasuwa masu fatauci sun hakura saboda rashin tabbas a kan lafiya da rayuwa, iyaye na fargabar tura ’ya’yansu zuwa makaranta.
Kashe-kashe da zub da jini da tashe-tashen hankula sun zamo ruwan dare a yankin Arewacin, lamarin da ya mayar da hannun agogo baya a dukkanin harkokin cigaba.
Satar dalibai a makarantu ta zama tamkar ruwan dare, a kullum babu abin da kafafen yada labarai ke ruwaitowa game da jiharka ta haihuwa sai an kashe mutane adadi kaza…, an kona gari kaza, an yi garkuwa da dalibai kaza da sauran abubuwa marasa dadi.
Allah Ya sa kana Aljanna Firdausi Malam Umaru, yau an wayi gari yankin Arewacin Najeriya musamman Jihohin Katsina da Kaduna da Zamfara na neman zama kufai saboda yadda matsalar tsaro ta addabe su.
Iyaye sun rasa ’ya’yansu, mata sun zama zawarawa, ’ya’ya sun zama marayu, kauyuka sun zama kufai, duk sakamakon gudun hijira da al’umma ke yi saboda masifar rashin tsaro.
Allah Ya kyauta makwancinka Malam Umaru Musa Yar’Adua, hakika ka yi kokarin inganta tattalin arzikin Najeriya, ta hanyar samar da isasshiyar wutar lantarki — da zummar farfado da masana’antun kasar nan, ’yan kasa su samu ayyukan yi — da inganta harkar sufuri ta hanyar samar da ingantattun hanyoyi.
Amma kash! Yanzu abin ba haka yake ba, saboda a kullum harkar wutar lantarki a kasar nan kara ci baya take yi, domin kullum kara zama a cikin duhu ake yi, hanyoyinmu sun zama tarkunan mutuwa, saboda rashin kyawu da inganci.
An wayi gari Najeriyar da kake fatan ganin ta shiga cikin manyan kasashe irinsu Brazil da Indiya wajen karfin tattalin arziki da cigaba, ta zama rikice-rikicin siyasa da addini da kabilanci da kuma rashin kwarewar shugabannin kasar sun sa tana neman komawa fagen yaki.
Rahotannin da ke fitowa daga sassan kasar nan babu dadin ji; daga an kashe mutane kaza, an kone caji ofis kaza, an kai hari gidan gwamnati kaza, an sace daliban makaranta kaza, an kashe jami’an tsaro da sauran abubuwan da ke mayar da hannu agogo baya.
Wasikar tawa cike take da labarai masara dadin ji ga mu da ke raye a nan duniya.
Amma babban labari mai dadi a gareka shi ne, tabbas ’yan Najeriya za mu ci gaba da alhinun rasuwarka Malam Umaru Musa Yar’Adua, musamman kasancewarka gwamna da shugaban kasa na farko a Najeriya da ka fara bayyana kadarorinka.
Hakan ya da kara tabbatar da kyamarka ga cin hanci da rashawa a tsakanin masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya.
Da ana kiranye lallai da mun yi maka, da ma an ce ba rabo da gwani ba… Kuma ga shi muna tuna bara, wanda hakan ke tabbatar da cewa ba mu ji dadin bana ba.
Amma za ka ji ni da wani sabon labarin nan gaba idan wasu abubuwa sun sauya.
Ina fatan za ka ci gaba da kasancewa cikin salama a Dausayin Rahamar Ubangiji.
Naka, Buhari Abba Rano, dan jarida kuma Mataimakin Mai Bincike a Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Ci gaban Al’umma CITAD, Kano.