A madadina da iyalina baki daya muna taya ka murnar samun nasarar cin zaben. Muna kuma yi maka addu’ar Allah ya sa jihar Kano ta sami ci gaban da bata taba samu ba a zamanin mulkinka.
Na zabi na aiko maka da budaddiyar wasika ne domin shawarwarin da na ke son zan baka, su kai gareka cikin sauki da kuma sauri kuma ina fatan na hannun damanka za su karanta wasikar, su kuma tunasar da kai yayin da ka shiga cikin gidan Gwamnati.
Ga shawarwarin kamar haka:
Yankunan karkara
Ina fata za ka kalli yankunan karkara ta fuskar samar musu da ababen more rayuwa domin daukewa babban birnin jiha cunkoso.
Na tabbata in ka zabi wasu kananan hukumomi da ke kauyuka ka samar musu da abubuwan ci gaba kamar Asibitoci ma su dauke da isassun magunguna da kwararrun likitoci, to ka daukewa ’yan’uwanmu na karkara wahalar zuwa Asibitin Murtala ko Sir Sunusi ko kuma Nasarawa da sauransu.
Kazalika ka samarwa yankunan karkara da manyan kasuwanni na zamani da hanyoyi da ruwan sha da hasken wutar lantarki da makamantansu, sannan ka yi kokarin sakarwa kananan hukumomi da kudadensu na ‘grant’.
Na tabbata in ka yi haka za ka ragewa babban birnin jiha cunkoso da nauye-nauyen da a yanzu suka haifar da matsala a jihar Kano.
Rarraba ayyukan gwamnati
Akwai bukatar ka fito da tsarin da a turance ake cewa ‘de-centralization of authority’ wato rarraba nauye-nauyen gudanar da Gwamnati daga sama zuwa kasa, misali a nan shi ne, idan ka tsara biya wa yara ‘scholarship’ ko kai su kasashen waje domin karatu, ko kuma in ka yi shirin bayar da jari ga Mata ko masu kananan sana’o’i, to yana da kyau ka bayar da dama a zabo wadanda suka cancanta tun daga matakin ‘ward’ zuwa Karamar hukuma zuwa jiha, ta haka ne za a taimaki jama’a tun daga tushe kuma shirin gwamnati zai dinga taba talakawa kai tsaye, amma idan aka ce wata hukuma ko wani kwamiti ne zai dinga gudanarwa da ire iren wadannan tsare-tsare shi kadai a matakin jiha, to ba za a cimma nasara yadda ya kamata ba.
Madatsun ruwa
Ya mai girma Gwamna, ina ganin zai yi kyau a kalli manyan Madatsun ruwan nan na Kano wadanda aka samar da su tun zamanin Audu Bako da nufin bunkasa noman rani da na damina, da aka yi shakulatin bangaro da su, tattare da cewa in aka ba su muhimmanci za su bunkasa tattalin arzikin manoma da makiyaya da ma na jihar baki daya.
Ayyuka masu karami da matsakaici da kuma dogon zango Ina ba da shawara gwamnati ta fito da manyan tsarukan da za su taimaki jihar Kano amma ta rarraba su zuwa kashi uku: wato gajere da matsakaici da kuma dogon zango.
Misalai
Gajeren zango; kamar kawar da Shara, samar da magunguna, samar da abinci ga dalibai da ire iren su, domin su wadannan suna cikin shirye-shiryen da a kullun ake bukatar su.
Matsakaicin Zango; kamar samar da guraren kwashe shara na dindindin musamman a birare, da biyan kudaden jarrabawar WAEC da NECO ko kuma kai dalibai kasashen waje da makamantansu, domin kuwa su wadannan ba kullun ake yinsu ba amma za a iya ganin alfanunsu ba da dadewa ba.
Dogon zango: Sune kamar samar da kamfanonin da za su sarrafa Shara domin su zama taki ko wani abin amfani kamar dai yadda ake yi a sauran kasashen duniya, haka ma giggina kananan Asibitoci.
Ina ganin idan an bi ayyukan gwamnati zango-zango to zai sa Gwamanati ta tafi a nitse ba tare da ta gigice har ta rasa me za ta yi ba.
Masarauta
Masarauta na da muhimmiyar gudanarwar da za ta bayar wajen samun nasarar shirye-shiryen gwamnati.
Wannan na nufin a dinga neman shawarar Masarauta musamman in za a zo da wani sabon tsari da ya shafi al’umma kai tsaye; misalin irin wadannan sune kamar matsalolin da suka shafi aure ko tarbiyyar matasa ko yaki da shaye-shaye ko dabanci da makamantansu.
Na tabbata Masarauta na da kyawawan shawarwari ga duk wadannan matsaloli da dangoginsu, kasancewar sarakunan gargajiya na kusa da Talakawa fiye da jami’an gwamnati.
Na fadi hakan ne domin akwai shirye-shiryen gwamnati da ba su sami nasara ba sai da aka hada da Masarauta; misali shirin nan na digon polio ba su sami karbuwa ba, sai da Sarki da Hakimai da Dagatai da ma su Unguwanni suka tallafa.
Hanyoyin sadarwa
Hanyoyin sadarwa na zamani na bukatar kulawa ta musamman domin ta zamarwa al’ummar wannan zamani alakakai, ma’ana dole rayuwa ba za ta yi wu ba sai an hada da hanyoyin sadarwa na zamani da na gargajiya, illa dai sai an fahimci alfanun da rashin alfanun da ke kunshe cikin hanyoyin sadarwar na zamani tukuna sannan za a ci gajiyarsu.
Kowa ya san daya daga cikin hanyoyin da ake shigar da fajirci da rashin tarbiyya tsakanin matasa ita ce ta danadalin sada zumunta na intanet.
Dan haka akwai bukatar a samar da cibiyar horaswa a kan wadannan dandalin domin koyarwa da wayar da kan matasa domin su gane cewa ba wai sakarci a ke yi a wadannan wurare ba, a’a, ana iya gudanar da kasuwancin da za a iya samun miliyoyin kudi idan an koyi yadda ake yi.
A nan ina baiwa mai girma gwamna shawarar cewa a sauya fasalin Hukumar tace fina-finai domin yi mata sabbin dokokin da za su dace da wannan zamani na ‘social media’ alabashi a shigar da batun cikin sabbin dokokin.
Yin hakan ya zama dole domin a yanzu akasarin dokokin Hukumar ba su dace da wannan zamani ba tunda an yi su ne a lokacin da babu kalubalen intanet.
Ibrahim Mandawari, [email protected]