A ci gaba da wasan kokawar da ake yi a gidan Kokawa na WAZOBIA da ke yankin Mil 12 a Jihar Legas, fitaccen dan kokawa Iliyasu Ligale daga kasar Nijer ya kayar da Shagon Taliya shi ma daga Nijar a turmi na farko da suka kara.
Babu shakka wasan ya kayatar saboda kasancewarsu kwararrun ’yan kokawa a Jihar Legas da kuma dabarun da suka nuna.
To sai dai wasan bai yi wa Shagon Taliya dadi ba saboda a turmi na farko Iliyasu Ligale ya kayar da shi ba tare da wani bata lokaci ba. Jim kadan da kammala wasan ne Iliyasu Ligale ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da ya taba yin kokawa da Shagon Taliya kuma shi ne karo na farko da ya samu nasara a kansa ba tare da ya ba shi wahala ba.
Shi kuwa Shagon Taliya cewa ya yi bai ji takaicin kayen da Lagale ya yi masa ba kuma a shirye yake ya sake kalubalantar sa a duk lolacin da ya shigo gidan kokawar. Hakazalika, Shagon dankanawa daga Najeriya ya kayar da Abdurrashid daga Nijar. Shi ma danbunza daga Nijar ya kayar da Yaro mai zamani daga Katsina. Haka ma Shagon Dogo daga Nijar ya kayar da Shagon Zage-zagi daga Zariya bayan sun ba juna wahala.
Shugaban gidan kokawar da ake yi masa lakabi da gidan WAZOBIA Drama and Film Production da ke gangaren Sa-idawa a yankin Mil 12 da ke Jihar Legas, Malam Sanda Zariya ya bayyana farin cikin sa da yadda wasan ya gudana. Ya ce ‘Na ji dadin yadda wasan ya kasance lami lafiya. Gaskiya wasannin sun kayatar sosai sai dai kokawar da ta fi burgewa ita ce wadda aka yi tsakanin shagon dankanawa da Abdurrashid. Saboda an yi zaton Abdurrashid zai kayar da dankanawa saboda ya fi karfinsa amma sai dankanawa ya nuna bajinta da iyawa ya kayar da Abdurrashin. Don har sai da Abdurrashid ya daga dankanawa sama amma ya kasa kayar da shi, gaskiya wasan ya burge sosai’.
Malam Sanda ya bayyana cewa suna daukar mataki iri-iri don tabbatar da tsaro a filin wasan tare da hana duk wani tashin hankali da ka iya tasowa.
Wasan Kokawa: Iliyasu Ligale ya yi wa Shagon Taliya mugun kaye
A ci gaba da wasan kokawar da ake yi a gidan Kokawa na WAZOBIA da ke yankin Mil 12 a Jihar Legas, fitaccen dan kokawa…