✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani yaro 1

Wani yaro ne kullum da dare sai ya lallava dakin kakarsa ya satar mata kudi a cikin zunguru. Idan ta ce wa ya daukar mata…

Wani yaro ne kullum da dare sai ya lallava dakin kakarsa ya satar mata kudi a cikin zunguru. Idan ta ce wa ya daukar mata kudi sai ya yi ta rantse-rantsen karya, cewa ba shi ba ne. Wannan sata da ake yi mata tana damun ta, rannan sai ta samo katuwar kunama, ta sanya a cikin zungurun nan, ta yi kamar tana barci. Gogan naka ya yi sallama ya ji shiru, sai ya danna hannunsa cikin zunguru da niyyar satar kudi kamar yadda ya saba. Kunama kuwa ta harbe shi. Ya kwala kara, ya ce: “Wayyo Allah, kunama ta harbe ni a zunguru!” Kakarsa ta fashe da dariya, ta ce: “Yau na kama varawona.”
Daga Ali Fancy Garko-Kano, 08171748500