Wani mutum mai shekara 52, Salihu Byezhe, ya yanke jiki ya faɗi yayin da ake Sallar Asuba a wani masallaci da ke ƙauyen Gudaba, a Ƙaramar Hukumar Kuje a Babban Birnin Tarayya, kuma daga baya ya rasu a asibiti.
Wani mazaunin yankin, Musa Dantani, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis bayan Byezhe ya yi sahur, ya yi alwala, sannan ya shiga masallaci don yin Sallar Asuba.
- Majalisar wakilai na shirin ƙwace rajistar jam’iyyu daga hannun INEC
- NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi
“Yayin da ake cikin sallah, kwatsam sai ya yanke jiki, nan take wasu daga cikin masu sallah suka riƙe shi suka kuma gaggauta kai shi asibiti.
“Lokacin da suke kan hanyar zuwa asibiti yana numfashi, amma da suka isa, ya rasu,” in ji Dantani.
Likitan a asibitin ya tabbatar da rasuwar Byezhe, inda ya danganta hakan da hawan jini.
Ɗaya daga cikin ’ya’yansa, wanda ke masallaci lokacin da abin ya faru, ya raka su asibiti, kuma ya ce likita tabbatar da rasuwasa.
Daga baya an gano Byezhe yana fama da matsalar hawan jini, wanda ya tashi yayin da ake sallar.
An yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 10:12 na safiyar ranar Alhamis bisa tanadin addinin Musulunci.