✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani mutum ya caka wa kananan yara 4 wuka a Faransa

Wani mutum ya far wa kananan yaran ’yan kimanin shekara uku, inda ya cacakka musu wuka a yayin da suke tsaka da wasa a safiyar ranar…

Wani mutum ya far wa kananan yaran ’yan kimanin shekara uku, inda ya cacakka musu wuka a yayin da suke tsaka da wasa a safiyar ranar Alhamis a kasar Faransa.

Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa biyu daga cikin yaran da wani babba wadanda dukkansu maharin ya daba wa wuka, suna cikin mawuyacin hali.

Hukumomin Faransa da farko sun sanar cewa mutum bakwai aka caka wa wuka, cikinsu har da kananan yara shida ne aka jikkata a harin na yankin Alps.

Gwamnatin kasar Birtaniya ta sanar cewa dan kasarta daya na daga cikin kananan yaran da aka daba wa wuka a harin.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, ya ce wadanda aka kai wa harin suna kwance rai kwakwai, mutu kwakwai, a yain da Ministan Harkokin Cikin Gida, Gerald Darmanin ya ce “jami’an tsaro sun yi nasara cafke maharan, domin ya fuskanci hukunci.