✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha

Kotu ta ce kada hukuncin ya yi tsaurin da zai hana aiwatar da ayyukan mazaɓar ɗan majalisa da aka dakatar.

Majalisar Dattawan Nijeriya ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Akpoti Uduaghan gabanin cikar wa’adin dakatar da ita da ta yi tsawon watanni shida.

Majalisar ta ce ala tilas ne dakatacciyar Sanatar ta bayar da hakuri tare da neman afuwa a hukumance gabanin cika umarnin da ta wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar na dawo da ita.

Shugaban Kwamitin Labarai da Harkokin Jamaa na Majalisar Dattawa, Sanata Adeyemi Adaramodu ne ya bayyana hakan yayin da yake martani kan hukuncin da kotun ta yanke a kan Sanata Natasha.

Ya yi bayanin cewa, a yayin yanke hukuncin da ta bayar da umarnin dawo da Sanata Natasha, kotun ba ta hana majalisar ladabtar da mambobinta a yayin da ta same su da laifi kamar yadda yake a cikin kundin tsarinta.

A bayan nan ne dai wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta buƙaci Majalisar Dattawan ta dawo da Sanata Natasha Akpoti.

Da take yanke hukunci, Mai Shari’a Binta Nyako ta kwatanta cewa dakatar da Natasha tsawon watanni shida da aka yi, ya yi tsauri.

Kotun ta kuma ce Shugaban Majalisar Dattawan Godswill Akpabio bai yi laifi ba, lokacin da ya hana Natasha yin magana a majalisa saboda lokacin ba ta zauna kan ainihin kujerar da aka ware mata ba.

Ta kuma buƙaci Sanata Natasha ta bai wa majalisar hakuri.

Sai dai a cewar kotun, tun da ’yan majalisa suna da tsawon kwanaki 181 don zama a kowane zango, dakatar da Natasha tsawon watanni da aka yi — yana kamar hana ta aiwatar da haƙƙokinta ne ga ’yan mazaɓarta na tsawon kwanaki 180.

Har ila yau, kotun ta ce Majalisar Dattawa tana da damar hukunta kowane ɗan majalisa da ya yi laifi, sai dai kada hukuncin ya yi tsaurin da zai hana aiwatar da ayyukan mazaɓar ɗan majalisa da aka dakatar.

Mai Shari’a Nyako ta kuma kori batun da Akpabio ya gabatar cewa kotun ba ta hurumin sauraron ƙarar.

Tun da farko, kotun ta ci Sanata Natasha tarar naira miliyan biyar saboda raina kotu, wanda ya hana ɓangarorin biyu yin magana a bainar jama’a kan batun.

Ta kuma buƙaci Natasha ta nemi afuwa a gidajen jaridu biyu da shafinta na Facebook cikin kwanaki bakwai.

A watan Maris ne Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha bayan da ta zargi Sanata Godswill Akpabio da cin zarafi na lalata, laifin da har yanzu ya musanta.