✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani mutum ya buɗe Ofishin Jakadancin Indiya na bogi a ƙasar

An gano ambasadan bogin a ofishin jakadancin nasa ne a cikin wani gidan haya a kusa da Delhi, babban birnin ƙasar

’Yan sanda sun kama wani mutum da ya buɗe Ofishin Jakadancin Ƙasar Indiya na bogi wani gidan haya, kuma yake gabatar da kansa a matsayin ambasadan ƙasar.

Jami’an tsaron sun kama mutumin mai suna Harshvardhan Jain ne a ofishin nasa da ke kusa da Delhi, babban birnin ƙasar, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito.

Sushil Ghule, Babban Jami’in Rundunar ’Yan Sanda ta Musamman a yankin Uttar Pradesh, ya ce an ƙwace motocin alfarma masu ɗauke da lambar Ofishin Jakadancin Indiya na bogi a hannun mutumin mai shekara 47.

Ya bayyana cewa ambasadan bogin yana damafarar mutane da alƙawuran samun aiki a ƙasashen waje; musamman inda yake iƙirarin zama Jakada ko Mashawarci ga ka kamfanoni irin su “Seborga” ko “Westarctica” da sauransu.

Ghule ya ce sauran kayan da aka kama Jain da su su haɗa da tambarin Ofishin Jakadancin Indiya da na wasu ƙasashe kimanin 40, duk na bogi.

An kuma kama tsabar kuɗi kimanin Dala dubu 52 (sama da Rupee miliyan 4.5 na Indiya) na kuɗaɗen kasashe daban-daban da aka yi wa ado da tutocin ƙasashen.

Kazalika an kama hotunan Jain da aka yi wa suddabaru aka hada shi da shugabannin duniya.

Ghule ya shaida wa kafar cewa ambasadan bogin yana fuskantar tuhume-tuhume da suka haɗa da zargin safarat kuɗaɗen Haram, yin ungulu da kan zabo, da kuma mallaka da amfani da takardun bogi.