An kama wani matashi da ake zargi da tono gawar kakarsa ta ɓangaren uwa tare da sare kanta da nufin yin tsafin kuɗi a Jihar Naje.
Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta kama mutumin mai shekaru 31 ne bayan dubansa ta cika a yankin.
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya cewa wanda ake zargin tare da abokansa da suka taimaka masa ya tabbatar musu cewa zai yi tsafin kudi ne da ƙwarangwal din tsohuwar.
A cewar kakakin rundunar wanda ake zargin ya furta cewa yana neman tsafin ne don biyan bashin da ya kai sama da Naira miliyan biyu.
- Ta’addanci: Alƙawuran sojoji 8 na kamo Bello Turji
- Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a Filato
A ranar 19 ga Yuli, 2025 ne jami’an ’yan sanda suka kama wannan gungun mutane da kai a otel ɗin Bida.
Babban wanda ake zargin ya tabbatar cewa kan kakarsa ce mai shekaru sama da 90 a lokacin da ta rasu kimanin shekaru biyu da suka gabata.
Ya ce da farko ya samo kan ne bisa umarnin wani boka, don neman kuɗi cikin hanzari. Amma, bayan jin sharuddan tsafin, ya kasa bi, sai ya ɓoye kan na tsawon shekaru biyu.
Daga baya, abokinsa da wani kuma sun yi masa tayin sayenkan a kan Naira 100,000, kuma suka biya Naira 40,000 a matsayin kuɗin kafin alƙalami.
Daga nan suka kai wani wanda ake zargi da ninka kuɗi, da ya nemi Naira 500,000 don yin tsafin kuma sun biya shi da kaɗan-kaɗan.
Bayan an gama aikin, ya umarce su kada su buɗe ganga har sai ya gaya musu.
Makonni sun shude babu labari ko kuɗi sai suka yi masa takakkiya zuwa gidansa, amma ya shawo kansu cewa su haɗu a wani otel a Bida inda za su karɓi kuɗinsu.
A otel din ne kuma ’yan sanda suka kama su gaba ɗayansu.