✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani kulob a katar ya taya Ighalo Naira biliyan 7

Wani kulob da ba a ambaci sunansa ba a katar ya nuna sha’awarsa kan saye dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake yi wa kulob…

Wani kulob da ba a ambaci sunansa ba a katar ya nuna sha’awarsa kan saye dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake yi wa kulob din Watford na Ingila kwallo Odion Ighalo a kan Yuro miliyan 13 kwatankwacin Naira biliyan 7 da miliyan 200.
Kamar yadda wani rahoto ya nuna, kulob din ya amince zai ajiye zunzurutun Yuro miliyan 13 ga Watford idan ya amince ya sayar masa da wannan dan kwallo.  Kulob din ya ce a shirye yake ya ba dan kwallon kwantaragin shekara hudu baya ga albashin Fam miliyan biyar kwatankwacin Naira biliyan biyu da Miliyan 300 a shekara.  Hakan ta sa dan kwallon zai samu albashin Yuro miliyan 20 ko Naira biliyan bakwai da miliyan 200 a tsawon kwantaragin shekara hudu.
Idan za a tuna kulob din Watford ya nemi sayar da dan kwallon ne tun a watan Janairun wannan shekara (2016) sai dai har aka rufe kakar saye da sayar da ’yan kwallo a wancan lokaci babu wani kulob da ya nuna sha’awarsa a kan dan kwallon.
dan kimanin shekara 26 Odion Ighalo an sha danganta shi da komawa kulob da dama da suka hada da West Ham United da Manchester United da Chelsea.
Ana sa rai kulob din Watford zai iya amincewa da tayin da kulob din katar ya yi masa ganin babu wani kulob da ya nuna zai iya sayen dan kwallon a kan irin wannan makudan kudi.