✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wani abu kan alkalin da ya mika Maryam Sanda ga hauni

Mai shari’a Yusuf Halilu, ne ya yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa ga Maryam Sanda kan kashe mijinta Bilyaminu Bello, ba bako ba ne wajen…

Mai shari’a Yusuf Halilu, ne ya yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa ga Maryam Sanda kan kashe mijinta Bilyaminu Bello, ba bako ba ne wajen karfin hali da jajircewa a bangaren yanke hukunci.

A ranar 15 ga Agustan bara ce, Mai shari’a Yusuf Halilu  ya daure mai sharhin nan a kafafen sadarwar zamanin, Ibrahim Garba Wala, wanda aka fi sani da IG Wala, tsawon shekara bakwai a gidan yari kan laifin bata suna da tunzura jama’a su yi bore ga tsohon Shugaban Hukumar Hajji ta Kasa, Barista Abdullahi Mukhtar.

Haka kuma a watan Nuwamban shekarar 2017, Mai shari’a Halilu ya yanke hukuncin zaman fursuna na shekara 35 ga daraktoci biyu a Ofishin Akanta Janar.

Hukumar EFCC ce ta yi karar mutanen bisa zargin cin amanar kasa da barnata Naira biliyan 1 ta hanyar amfani da wasu kamfanoni.

A ranar 1 ga Maris din shekarar 2016, lokacin da aka ba shi shari’ar tsohon madugun tsohon Shugaba Kasa Goodluck Jonathan, Kanar Ojogbane Adegbe wanda Hukumar EFCC ta tsare watanni ba tare da gabatar da shi a kotu ba, Mai shari’a Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda Hukumar EFCC ta zama wajen ajiye marasa laifi na sojoji. Duk da cewa da farko EFCC ta ce tana bincikar Adgebe ne bisa zargin almundahana wajen sayo makamai. Ta kara da cewa Rundunar Soji ce ta bukaci a tsare shi. Nan Mai shari’a Yusuf ya ce sun saba wa sashi 36 na Tsarin Mulkin 1999, wanda ya ce wanda ake zargi mara laifi ne, har sai kotu ta tabbatar da laifinsa.

A watan Maris din 2016, Mai shari’a Halilu ya caccaki Hukumar EFCC da Rundunar Sojin inda ya ce suna aiki kamar jahilai wajen tsare mutane tsawon lokacin ba tare da bayar da beli ba, kan batun Kanar Sambo Dasuki da Kanar Nicholas Ashinze, inda a lokacin ya ce, “Doka ce ta kafa Hukumar EFCC. Don haka kotu ba za ta bari ta rika aiki kamar ta fi karfin doka ba. Ya kamata a lura da cewa taken hukumar shi ne babu wanda ya fi karfin doka, amma su suna aiki kamar sun fi karfin doka.

“Dokokin EFCC ba su fi karfin Dokokin Tsarin Mulkin Najeriya ba. A nan masu gabatar da jawabi ba su nuna cewa mun samu ci gaba ba. Suna abu kamar muna mulkin kama-karya na sojoji, inda za su iya kama mutum kuma su sake lokacin da suka gadama. Dole in rufe ido in bayyana cewa Hukumar EFCC da Rundunar Sojin Najeriya sun yi aiki kamar jahilai,” inji shi.

An haifi Mai shari’a Halilu a ranar 15 ga Agustan 1972 a Karamar Hukumar Nasarawan Eggon da ke Jihar Nasarawa.

Ya yi karatun lauya a Jami’ar Jos a 1997, sannan ya je Makarantar Kwararewa a Aikin Lauya a 1998.

Ya yi Digiri na biyu a shekarar 2001 a Jami’ar Jos. Bayan ya dade yana aiki a matsayin lauya  mai zaman kansa, a shekarar 2010 ne Mai shari’a Halilu Yusuf ya Alkalin Babbar Kotun Abuja.

Yana da aure da ’ya’ya.