✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wakar Sani Danja ta ja hankali a Twitter

Masu mu’amala da shafin sada zumunta na Twitter sun yi tsokaci sosai a kan wata sabuwar waka da jarumin fina-finan Hausa, Sani Danja ke shirin…

Masu mu’amala da shafin sada zumunta na Twitter sun yi tsokaci sosai a kan wata sabuwar waka da jarumin fina-finan Hausa, Sani Danja ke shirin kaddamarwa.
Wakar, mai suna As E Dey Do Me a cikin Ingilishi, ta dauki hankalin ma’abota shafin sada zumuntar ne saboda an yi amfani da harshen Hausa da Ingilishi a cikinta.
Sani Danja ya shaida wa BBC cewa wakar ta yi masa ba-zata, yana mai cewa bai yi tsammaci za ta ja hankalin jama’a haka ba.
Wakar dai ta fi karkata ne ga Ingilishi maimakon Hausa, amma mawakin ya ce idan kana son ka karbu a wurin masu saurare kakan tafi ne a hankali, da ka karbu a inda kake so, to za ka iya amfani da harshenka zalla kuma mutane za su karbi abin hannu bibbiyu ba tare da duba ga harshen ba.
A cikin wakar, Sani Danja ya bukaci masu saurarensa su dogara ga Allah, yana mai cewa duk wata hanya da mutum ya bi idan ba ta Ubangiji ba ce ba ta bullewa.
Wasu dai na ganin yawancin wakokin Sani Danja ba sa nuna al’adun Bahaushe, musamman ta fuskar suruta da kalami, inji rahoton na BBC.
Sai dai mawakin ya musanta hakan, yana mai cewa ba sutura ce a bar kallo ba, darasin da wakar ta kunsa shi ne mai muhimmanci.
Ya kara da cewa wasu daga cikin wakokin da ya yi da takwarorinsa da ke Kudu sun kwaikwayi suturar Hausawa, misali babbar riga da hula.