Abin da ake cewa Layya shi ne duk wata halastacciyar dabba da aka yanka domin neman kusanci ga Allah.
Layya tana da asali a cikin Kur’ani da Hadisin Annabi (SAW). A cikin Kur’ani Allah (TWT) Yana cewa: “Ka yi Sallah ga Ubangijinka kuma ka yi yanka.” (Kausar: 2).
A Hadisi kuwa Anas bin Malik (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya yi layya da raguna biyu bakake, masu kahonni.
Ya yanka su da hannunsa, ya yi bisimillah ya yi kabbara, ya kwantar da su ta gefen wuyansu” (Muslim ya ruwaito).
Akwai Hadisai masu yawa a kan layya inda a shekara ta biyu Bayan Hijirar Annabi (SAW) aka shar’anta yin layya.
Ita layya Sunna ce mai karfi, tana hawa kan wanda ya cika sharudda masu zuwa:
1. Ya kasance da ba bawa ba, a nan ba batun namiji ko mace. Tana zama Sunna a kan mutum ga kansa da iyayensa, idan talakawa ne da ’ya’yansa maza idan ba su balaga ba da ’ya’yansa mata idan ba su yi aure ba.
Ba Sunna ba ce a kan mutum ya yanka wa matarsa ko dansa da aka haifa a Ranar Layyar.
2. Kada ya kasance mahajjaci, domin shi mahajjaci, hadaya ce a kansa.
3. Ya zama ba matalauci ne ba. Ma’ana kada ya zama yana buqatar kudin yin Layyar domin biyan wasu buqatu nasa.
Amma idan zai iya cin bashi ya yi Layyar, to ya yi, idan ya san zai iya biya, ba tare da takura ba. Wadansu malaman sun ce kada mutum ya ci ba shi domin ya yi Layya.
Dabbobin da ake yin Layya da su Dabbobin da ake yin layya da su kadai su ne: Rakumi da sa da rago da taure da matansu.
Rago sai wanda ya shekara, taure kuwa sai ya shiga shekara ta biyu. Sa kuma sai wanda ya kai shekara uku. Shi kuwa rakumi sai ya kai shekara biyar.
A wajen Layya, rago ya fi falala (sai tunkiya), sai taure (sai akuya), sai kuma sa (sai saniya). Bayan sa sai kuma raqumi (sai taguwa).
A cikin kuma dukkan dabbobin da aka ambata an fi fifita mazansu a kan matansu, lafiyayyunsu (wadanda suke iya yin barbara) kuma a kan fidiyayyunsu (wadanda ba sa iya yin Barbara saboda an dandake su).
Sai dai idan fidiyayyun sun fi kitse ne sai a yi da su.
Sharuddan ingancin Layya
1. Dole ne a yi yanka da rana, ba ya inganta a yi shi da daddare. Rana tana farawa ne daga ketowar alfijir.
Amma a game da Layya sai liman (shugaba) ya yanka tasa Layyar sannan kowa zai yanka tasa.
Ba wai da an wayi gari ne kawai sai a yi ta yanka ba, abo haka idan mutum ya yanka kafin liman ya yanka tasa, layyarsa ba ta yi ba.
2. Mai yin yanka dole ne ya zama Musulmi, yankan kafiri bai halatta ba. Koda kuwa ma’abocin littafi ne (AhlulKitabi.” Amma ya halatta a ci yankan ma’abocin littafi.
3. Kadaituwa da sayen dabbar Layyar. Ba ya halatta mutane da yawa su hadu a cikin kudin dabbar Layya daya.
In kuma suka hada kudi suka sayi dabba suka yanka, ba ta zama Layya ba.
Amma idan daya daga cikinsu ya biya saura kudinsu, shi ya kadaita da dabbar, a wannan lokaci ya halatta ya yi Layya da ita.
Duk da haka ya halatta ga mai yin layya ya sanya wani ko wadansu a cikin ladan Layyar, kafin ya yanka, ba bayan ya yanka ba. Koda kuwa wadanda zai sa a cikin ladan sun wuce bakwai.
Yin hakan kuma sai da sharudda uku:
a) Ya kasance wanda zai saka cikin ladan na kusa da shi ne. kamar da ko dan uwa ko dan ammi ko matarsa.
b) Ya kasance wanda zai shigar cikin ladan layyar, wanda ciyar da shi ya wajaba a kansa ne. Ko kuma dai shi yake ciyar da shi. Wato ko ba don ciyar da shi din ya wajaba a kansa ba.
c) Ya kasance suna zaune tare a gida daya.
Idan wadannan sharudda suka tabbata, layya ta fadi daga kan wanda aka shigar cikin Layyar wani din.
Ana bukatar wadannan sharudda ne idan zai shigar da wadansu mutane cikin layyarsa.
Amma idan su kadai zai yi wa Layya a ware ban da shi a ciki, ya inganta ya yi.
Ba sai da cikar wadancan sharudda da aka ambata ba. Ya halatta a yi gamayya a cikin Layya idan dabbar Layyar ta zama raqumi ko saniya. Sannan kuma kada adadin masu gamayyar ya wuce bakwai.
Idan suka wuce bakwai, bai halatta su yi gamayya a dabba daya ba. Dalili a nan shi ne Hadisin Jabir (RA) da yake cewa: “Mun yi Layya tare da Manzon Allah (SAW) a Shekarar Hudaibiyya, kowace taguwa mutum bakwai, saniya ma mutum bakwai” (Muslim ya ruwaito).
4. Dole ne dabbar Layyar ta kasance ta kubuta daga cututtuka ko aibubbuka da suke a fili. Saboda Hadisin da Barra’u (RA) ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya mike tsaye a cikinmu ya ce: “Dabbobi hudu ba ya halatta a yi layya da su.
Mai ido daya wadda rashin idon ya fito fili ko marar lafiya, wadda rashin lafiyar ta fito fili.
Gurguwa, wadda gurguntakarta ta fito fili, wadda ta karye a kafa da kuma wadda ba ta da bargo” (Abu Dauda ya ruwaito).
Akwai kuma Hadisin da aka ruwaito daga Aliyu (RA) cewa: “Annabi (SAW) ya hana a yi Layya da dabba mai gutsurarren kunne da gutsurarren kaho” (Abu Dauda ya ruwaito).
Haka ba za a yi da mai gutsurarriyar kafar gaba ko ta baya ba, ko marar ji ko mai warin baki ko wadda ba ta yin kuka ko marar bargo ko mai gutsurarren bindi ko marar lafiya da rashin lafiyarta ya fito fili ko mahaukaciya, madauwamin hauka, ko gurguwa ko ramammiya da ramarta ta fito fili.
Dukkan abubuwan da aka ambata a baya, idan masu sauki ne, babu laifi a yi Layya da ita.
Haka bai halatta a yi Layya da dabbar da kahonta ya karye yake yin jini ba. Ko wadda kashi daya daga cikin uku na bindinta ya gutsure, sai dai idan wanda ya gutsure bai kai kashi daya cikin uku ba, babu laifi.
Haka kuma wadda ta rasa hakora biyu ko fiye domin yarinta ko tsufa ba za a yi Layya da ita ba. Amma idan hakori daya ne ta rasa, babu laifi.
Haka idan fiye da kashi daya cikin uku na kunnenta ya tsage ba a Layya da ita.
Kubutar dabba daga dukkan aibobin da aka ambata sharadi ne na ingancin Layya.
Idan mai yin Layya bai lura da wani aibi da yake jikin dabbar layyarsa ba, sai bayan ya yanka, sai ya yi sadaka da kudin lamunin da zai amso daga wajen wanda ya sayar masa da dabbar ko kuma kimar kudin lamunin.
Domin ita Layya sai an yanka ta take wajaba. Ba ta wajaba da niyya ko warewa.
Lokacin yanka Layya
Lokacin yankan Layya yana farawa ne daga lokacin da liman ko shugaba ya yanka tasa dabbar Layyar.
Shi kuwa liman zai yanka dabbar layyarsa ce bayan ya sallame Sallar Idi, bayan gama hudubarsa.
Idan kuma liman ba ya da abin da zai yi Layya, in ya gama Sallah da huduba sai ya umarci jama’a kowa ya je gida ya yanka abin layyarsa.
Wadanda ba su kusa da masallaci kuma sai su kintaci daidai lokacin da ya isa a ce limamin ya gama yanka layyarsa, in da a ce zai yi Layyar, sai su yanka.
Lokacin yin yankan yana zarcewa har zuwa faduwar ranar kwana ta uku daga kwanakin yanka. Dalili kuwa shi ne Hadisin da Barra’u (RA) ya ruwaito ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya yi yanka bayan an yi Sallah ya cika yankarsa, kuma ya dace da Sunnah” (Buhari ya ruwaito).
Akwai kuma wanda Jundubi bin Sufyan Al-Bajli ya ruwaito cewa: “Na kasance tare da Annabi (SAW) a ranar yanka, sai yake cewa: “Wanda duk ya yanka kafin a yi Sallah, to, ya yanka wata a madadinta, wanda kuwa bai yanka ba, to, ya yanka.” (Buhari ya ruwaito).
Kuma wanda a lokacin yankan da aka ambata a sama ya kubuce masa, ba zai yi ramuwar yanka a wani lokaci ba.
Idan liman ba tare da wani uzuri ba, ya yi jinkirin yanka layyarsa, sai a dan saurara gwargwadon lokacin da zai isa a yi yankar bayan gama Sallah, sai kowa ya yanka layyarsa.
Idan kuwa akwai uzurin da ya sa ya jinkirta yanka Layyar tasa, sai jama’a su saurare shi har zuwa kusa da zawali, ta yadda gwargwadon yankan ne kawai zai saura ga zawali, sai kowa ya yanka layyarsa.
Idan ba a yin Sallar Idi a gari, sai mutanen garin su kintaci idar da Sallah da hudubar gari mafi kusa da su.
Sannan kuma babu wani laifi a tare da su, koda ta bayyana cewa sun riga limamin wancan gari da suka kintata don yin Layyar.
Abin so ga mai yin Layya
1. Ya jinkirta aske duk wani gashi daga jikinsa da kuma jinkirta yin yankan farce har zuwa bayan ranar 10 ga watan Zul-Hajji (watan Babbar Sallah), daga zarar wata ya kama har sai ya yi Layya.
Duk daya ne ko shi ne zai yi Layyar ko za a saka shi cikin ladanta ne. Saboda Hadisin da Ummu Salma (RA) ta ruwaito cewa Annabi (SAW) ya ce: “Idan goma (ga watan Zul-Hajji) ta shiga, alhali kuma dayanku yana da niyar yin Layya, kada ya shafi wani abu daga gashin jikinsa.” (Muslim ya ruwaito)
2. Ya yanka abin layyarsa da kansa. Wannan kuma duk daya ne ko mai yin Layyar namiji ne ko mace ko yaro, saboda yin koyi da Annabi (SAW). An karbo daga Anas (RA) cewa “Manzon Allah (SAW) ya yanka taguwoyi guda bakwai da hannuwansa a tsaye” (Abu Dauda ya ruwaito).
Abin ki ne mutum ya wakilta wani ya yanka masa, matukar zai iya yankawa da kansa.
3. Ya hallata mutum ya ci, ko ya yi sadaka, ya kuma yi kyauta da naman layyarsa, ba tare da iyakancewa ba.
4. Ya yanka dan dabbar layyar tasa, idan ya fito daga gare ta kafin ya yanka ta. Amma idan dan ya fito bayan an yanka uwarsa, wannan hukuncinsu daya da ita.
5. An so magaji ya aiwatar da Layyar wanda ya gada, matukar dai ya nuna ta kafin rasuwarsa.
Abubuwan da ba a so mai yin Layya ya yi
1. Aske gashin dabbar Layyar kafin a yanka ta. Saboda yin hakan zai rage wa dabbar kyau.
2. Sayar da wannan gashi da aka ce kada a aske daga jikin dabba idan har an riga an aske din.
3. Shan nonon dabbar Layyar ta tasa.
4. Ciyar da kafiri daga naman Layyar.
5. Abin ki ne a yi wa mamaci Layya. Sai dai idan tun kafin ya rasu ya nuna dabbar layyar tasa.
6. Abin ki ne a musanya dabbar Layyar da wadda ba ta kai ta girma ko lafiya ba.
Allah Ya sa mu dace, Ya kuma karbi ibadunmu.
Muntasir Umar Fagge, ya rubuto ne daga Kano, kuma za a iya samun sa ta: 08037747019