Wani dan Uganda mai suna Henry Dhabasani wanda yake goyon bayan kulob din Arsenal da ke Ingila ya rasa gidansa a wata caca da ya yi da abokinsa mai suna Rashid Yiga mai goyon bayan kulob din Manchester United da ke Ingila.
Mutanen biyu sun yi cacar ce kafin a buga wasan Arsenal da United a gasar rukunin Premier kimanin makwanni biyu da suka wuce.
An ce Henry Dhabasani ya sha alwashin sanya gidansa mai dakunan kwana biyu watau (two bedrooms flat) yayin da shi kuma Rashid Yiga ya sanya motarsa da matarsa.
Rahotannin da jaridar The Obserber da ake wallafata a Uganda ta ce mutanen biyu sun kulla yarjejeniyar ce a rubuce kuma a gaban jama’a don su zama shaida.
Waiwayen Harkokin Wasanni A Shekarar 2013: Wani ya rasa gidansa a caca a wasan Manchester United da Arsenal
Wani dan Uganda mai suna Henry Dhabasani wanda yake goyon bayan kulob din Arsenal da ke Ingila ya rasa gidansa a wata caca da ya…
