✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Waiwayen Harkokin Wasanni A Shekarar 2013: Messi ya sake lashe gwarzon dan kwallon duniya a karo na hudu a jere

Shahararren dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen dan kasar Ajantina Lionel Messi ya sake kafa sabon tarihi a fagen kwallo.  A wannan karo ya…

Lionel Messi rike da kofin Gwarzon Dan kwallon Duniya a karo na hudu a jereShahararren dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen dan kasar Ajantina Lionel Messi ya sake kafa sabon tarihi a fagen kwallo.  A wannan karo ya sake lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya na shekarar 2012 ne a karo na hudu.  An bayyana shi a matsayin wanda ya lashe kyautar ce a ranar Litinin da ta gabata a hedkwatar hukumar FIFA da ke Zurich a Swaziland a wani kasaitaccen bikin da hukumar kan shirya a duk shekara.
Ya doke abokan takararsa Cristiano Ronaldo dan kulob din Real Madrid ne da kuma Andres Ineista dan kulob din FC Barcelona.