✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Waiwayen Harkokin Wasanni A Shekarar 2013: Carlo Ancelloti ya zama kocin Real Madrid

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayyana Carlo Ancelotti, tsohon kocin kulob din PSG da ke…

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayyana Carlo Ancelotti, tsohon kocin kulob din PSG da ke Faransa a matsayin sabon kocinsa.
A shekaranjiya Laraba ne kuma kulob din ya yi bikin kaddamar da kocin a bainar jama’a a harbar filinsa da ake wa lakabi da Santiago Bernabeu.
Ancelotti wanda ya samu nasarar lashe kofin zakarun kulob-kulob har sau biyu (UEFA Champions League) a shekarar 2003 da 2007 a lokacin da yake horarwa a kulob din AC Milan da ke Italiya ya samu nasarori da dama a kulob daban-daban. Ya taba lashe kofunan European Cup sau biyu baya ga lashe gasar rukuni-rukuni da ya yi a Italiya da Ingila da kuma a Faransa.