Babbar sallah ta zo da abun mamaki, inda aka wayi gari masarautar Daura ta yi wa dan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari nadin sarauta.
Yusuf Buhari, wanda ya ke da namiji tilo ga Shugaba Buhari, ya ziyarci Daura don gudanar da bikin babbar sallah, amma ya yi gamo da katar.
Sarkin Daura, Mai Martaba Farouk Umar Farouk, ya yi wa matashin nadin sarautar ‘Talban Daura’ kamar yadda Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasa ya sanar a ranar Talata.
Sai dai ana ganin wannan lamari ya kasance tamkar maimai ko kuma mantuwa ta ajizanci irin na dan Adam daga bangaren sarkin, inda shekaru biyu da suka gabata ya bayar da sarautar ta Talban Daura ga Shugaba Alpha Conde na Kasar Guinea.
A shekarar 2019 ce sarkin na Daura ya yi wa Shugaba Conde nadin sarautar ‘Talban Daura’.
“Na nada ka sarautar ‘Talban Daura’ sakamakon rakiyar da ka yi wa danmu shugaban kasa Muhammadu Buhari don gudanar da sallah babba a garin Daura.
“Talban-Daura sarauta ce da aka yi wa Shugaba Conde, don haka muna godiya da wannan ziyara,” a cewar Farouk.
A watan Agsutan 2019 ne Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina, ya wakilci Shugaba Buhari yayin nada Shugaba Conde sarautar Talban Daura.
A wancan lokaci ne Gwamna Masari ya mika godiya ta karamcin da aka Shugaba Conde a madadin Shugaba Buhari.
Nada Yusuf Buhari Talban Daura
Masarautar Daura ta nada dan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Yusuf a matsayin Talban Daura.
Sarkin Daura ya ba wa Yusuf Buhari sarautar Talban Daura ne a jiya Talata da ta kasance ranar Sallah babba, kamar yadda mai magana da yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu ya sanar.
“Ina tare da Yusuf Buhari, wanda ba da jimawa ba aka ayyana a matsayin Talban Daura da kuma Danmadamin Daura, Musa Daura’ kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya sanya hotonsa da matasan su biyu.
Sarautar Talba, babbar sarauta ce a Masarautar Daura, wadda Sarki Umar Farouq yake jagoranta.
Musa Daura, da ne ga Shugaba Muhammadu Buhari, kuma shi ne Danmadamin masarautar a cewar Garba Shehu.
Tun makon jiya Shugaba Buhari ya je mahaifarsa da ke Daura a Jihar Katsina, inda ya kammadar da wasu ayyuka, yake kuma hutun Sallah.