✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Waiwaye: Sau nawa aka taba yin juyin mulki a Nijar?

Wasu sojojin Nijar sun yi wa Shugaban Kasar, Mohammed Bazoum juyin mulki ’yan sa’o’i baya masu tsaron Fadar Shugaban sun tsare shi a cikinta a…

Wasu sojojin Nijar sun yi wa Shugaban Kasar, Mohammed Bazoum juyin mulki ’yan sa’o’i baya masu tsaron Fadar Shugaban sun tsare shi a cikinta a ranar Laraba.

Kakakin sojojin, Kanal Amadou Abdramane, ya ce sun yanke hambarar da gwamnatin Bazoum ne “saboda kawo karshen raunin shugabanci da kuma matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.

Kanal Amadou ya kuma ce sun sanya dokar ta-baci a duk fadin kasar sannan sun rufe dukkan iyakokinta sannan an rushe dukkan hukumomin gwamnati.

Sai dai Bazoum ya wallafa a dandalin Twitter cewa za su ci gaba da fafutuka don ganin sun kare Dimokuradiyyar da ’yan kasar suka yi aikin kafawa.

Bazoum

Ga jerin lokutan da aka taba samun juyin mulki a kasar ta Nijar:

1974

A watan Afrilun 1974 Laftanar Kanal Seyni Kountche, ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen mulki Diori Hamani na shekara 14.

Daga nan ne shugaban ya kafa Majalisar Koli ta Sojojin kasar mai mambobi 12, wacce ta jagoranci kasar a gwamnatinsa.

A cewar wasu rahotannin a lokacin, an kashe kusan mutum 20 a zamanin juyin mulkin.

Sojojin da suka yi juyin mulki a 1974

1996

Jami’an sojoji sun shirya juyin mulkin ne inda suka kawar da gwamnatin Shugaba Mahamane Ousmane da Fira Minista Hama Amadou a watan Janairun 1996, inda suka yi wukar kugu da cewa gwamnatin ta jefa tattalin arzikin kasar cikin tsaka mai wuya.

Sai dai matakin nasu ya fusata kasar da ta taba yi wa Nijar din mulkin mallaka, wato Faransa.

Tsohon Shugaban mulkin Soja na Nijar, Kanal Ibrahim Ba’are Mainasara

Laftanar Janar Ibrahim Ba’are Mainasara, Shugaban Sojojin Kasar ne ya dare mulki, yana mai cewa sun yi juyin mulkin ne domin sake habaka tsarin Dimokuradiyya na jam’iyyu masu yawa, ba wai su wargaza shi ba.

1999

Sai dai wasu sojojin masu tawaye sun kashe Ba’are Mainasara yayin wani harin kwanton bauna a filin jirgin sama na Yamai, lamarin da ya share fagen juyin mulki karo na uku a tarihin kasar.

Daouda Malam Wanke, Kwamnandan jami’an tsaron Fadar Shugaban Kasa ne ya jagoranci gwamnatin a lokacin, kafin daga bisani ya sanar da cewa za a yi zabe tare da dawo da mulkin farar hula a shekara ta 2000.

Mamadou Tandja ne ya lashe zaben da aka shirya, inda ya doke tsohon Fira Ministan Kasar, Mahamadou Issoufou. Masu sanya idanu sun bayyana zaben a matsayin sahihi.

2010

Tawagar wasu sojoji da suka kira kansu masu yunkurin dawo da mulkin Dimokuradiyya (CSDR), karkashin jagorancin Janar Salou Djibo, suka kama tare da tsare Tandja da Ministocinsa.

Lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnatin Tandja a 2010

Sojojin sun kuma dakatar da Kundin Tsarin Mulkin kasar tare da rushe dukkan hukumomin gwamnati.

Sojojin dai sun sha alwashin dawo da kasar kan tafarkin Dimokuradiyya na hakika, bayan sun zargi Tandja da gyara Kundin Tsarin Mulkin.

2023

A ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, jami’an tsaron Fadar Shugaban Kasa karkashin Janar Omar Tchiani, suka kulle Shugaba Mohammed Bazoum a cikin fadar, lamarin da ya sha suka daga kasahen duniya daban-daban.

Sojojin dai sun sanar da rushe dukkan hukumomin gwamnati sannan sun rufe dukkan iyakokin kasa da na sama tare da sanya dokar ta-baci a fadin kasar.

Ministan Harkokin Wajen Njar, Hassoumi Massoudou, ya yi kira ga sojojin da su saki Bazoum sannan a tattauna bukatunsu cikin ruwan sanyi.