✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wainar da za a toya ranar Talata a Gasar Zakarun Turai

Paris St Germain za ta fafata da Bayern Munich ranar Talata a wasan farko zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a Gasar Zakarun Turai. Bayern…

Paris St Germain za ta fafata da Bayern Munich ranar Talata a wasan farko zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a Gasar Zakarun Turai.

Bayern za ta buga wasan ne, bayan karawa 19 a jere ba a doke ta ba – har da lashe wasa uku da ta buga a bayan nan.

Kungiyar Jamus ta kawo wannan matakin, bayan cin dukkan karawa shidan da ta yi a Gasar Zakarun Turai a kakar nan.

PSG da Bayern Munich sun sha haduwa a zagayen ‘yan 16 a Gasar Zakarun Turai.

Kaka ta 11 da PSG ke zuwa matakin ‘yan 16 a Gasar Zakarun Turai, Real Madrid da Bayern ne ke gabanta a wannan kwazon.

Rabon da Bayern ta kasa zuwa irin wannan matakin tun kakar 2007/08, ita kuwa Real kan je zagayen ‘yan 16 tun da aka kirkiro gurbin a 2003/04.

Sai dai karo hudu ana fitar da PSG daga wasa shida baya a zangon ‘yan 16, ita kuwa Bayern sau daya ta kasa kai wa kwata-final daga fafatawa 10 a baya shine a 2018/19.

Bayern ta ziyarci Faransa ba tare da Sadio Mane da Lucas Hernández da Noussair Mazraoui da kuma Manuel Neuer, wadanda ke jinya.

Ryan Gravenberch ya warke, bayan da bai yi mata karawa da Wolfsburg da Bochum ba, Joshua Kimmich zai buga fafatawar, bayan dakatar da shi a Bundesliga.

Kyalian Mbappe wanda ya ci kwallo bakwai a cikin rukuni a Zakarun Turai a bana ya murmure, wanda aka ce zai yi jinya mai tsawo tun farko.

Kyaftin din Argentina, Lionel Messi yana cikin ‘yan kwallon da PSG ta bayyana da za su kara da Bayern ranar Talata.

Tsohon dan kwallon Bayern, Renato Sanches wanda ke taka leda a PSG na yin jinya.

Kungiyoyin sun kara a Zakarun Turai sau 11, inda PSG ta ci karawa shida, ita kuwa Bayern ta yi nasara a biyar.

Wasa 11 baya da aka kara tsakanin kungiyoyin biyu:

2020/2021

Zakarun Turai

Paris St-G. 0 – 1 Bayern Munich

Zakarun Turai

Bayern Munich 2 – 3 Paris St-G.
2019/2020

Zakarun Turai

Paris St-G. 0 – 1 Bayern Munich
2017/2018

Zakarun Turai

Bayern Munich 3 – 1 Paris St-G.

Zakarun Turai

Paris St-G. 3 – 0 Bayern Munich
2000/2001

Zakarun Turai

Bayern Munich 2 – 0 Paris St-G.
Champions League

Paris St-G. 1 – 0 Bayern Munich
1997/1998

Zakarun Turai

Paris St-G. 3 – 1 Bayern Munich

Zakarun Turai

Bayern Munich 5 – 1 Paris St-G.
1994/1995

Zakarun Turai

Bayern Munich 0 – 1 Paris St-G.

Zakarun Turai

Paris St-G. 2 – 0 Bayern Munich

Tottenham da AC Milan

A daya bangaren kuma, AC Milan za ta kara da Tottenham a San Siro a Gasar Zakarun Turai ranar Talata a wasan ‘yan 16 da suka rage a gasar.

Tottenham tana ta biyar a teburin Firimiyar Ingila da maki 39, ita kuwa Milan mai maki 41 tana ta shida a teburin Serie A.

Milan tana da Kofin Zakarun Turai bakwai jimilla, ita kuwa Tottenham na fatan daukar na farko a tarihi.

Antonio Conte ya koma jan ragamar Tottenham bayan jinya da ya yi, sai dai kungiyar ta sha kashi da ci 4-1 a hannun Leicester City a Firimiyar Ingila ranar Asabar.

Kungiyar da ke buga Firimiyar Ingila za ta kara da Milan ba tare da kyaftin Hugo Lloris ba, wanda ke jinyar wata biyu.

An dakatar da Pierre-Emile Hojbjerg, yayin da Rodrigo Bentancur zai yi jinya zuwa karshen kakar bana.

Dan wasan tawagar Uruguay ya ji rauni a fafatawar da Leicester City ta casa Tottenham a King Power.

Wani dan kwallon Tottenham da ba zai yi mata wasan da ta ziyarci Italiya shi ne Yves Bissouma, wanda ke bukatar likitoci su yi masa aiki a kafarsa ta dama.

Saboda haka Conte ya ce zai yi amfani da matashin dan wasa mai shekara 22, Oliver Skipp da Pape Matar Sarr, mai shekara 20 a gurbin tsakiya.

Wannan shi ne wasa na biyar da za su fafata a tsakaninsu a gasar Zakarun Turai, inda Tottenham ta ci biyu da canjaras biyu.

Wasannin da suka buga a tsakaninsu:

Kakar 2010/2011

Champions League

Tottenham 0 – 0 Milan

Champions League

Milan 0 – 1 Tottenham
1971/1972

UEFA CUP

Milan 1 – 1 Tottenham
UEFA CUP

Tottenham 2 – 1 Milan

%d bloggers like this: