An samu dogayen layuka a gidajen mai a yayin da zaman lafiya ya dawo a Gombe bayan zanga-zangar tsadar rayuwa.
Dogayen layukan man na da nasaba da rashin budewar yawancin gidajen mai sakamakon fargaba da zaman dardar da kuma zargin yiwuwar dawowar zanga-zangar a jihar.
Farashin man yana N850 a ’yan gidajen man da suka bude, ga kuma karancinsa a mafi yawancin gidajen.
Wakilinmu ya zaga cikin garin Gombe, idan ya lura gidajen mai kadan ne suke da shi, lamarin da ya sa wasu masu ababen hawa gwamnace su saya tsada a wurin ’yan bumburutu a kan N1,200 kowce lita.
- DAGA LARABA: Yadda Za Ku Gane Shafukan Tallafin Gwamnati Na Bogi
- Ƙura ta lafa a yankunan da aka sa dokar hana fita a Yobe
Wasu masu ababen hawa da wakilinmu ya zanta da su a wani gidan mai sun bayyana cewa karancin man ya jawo hakan sakamakon shiga zanga-zanga da aka yi, wasu kuma na ganin kamar za a sake komawa zanga-zangar
Mutanen sun yi kira ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya tausaya wa al’umma ya dawo da tallafin mai da aka cire saboda ’yan ƙasar suna cikin halin kunci da tsadar rayuwa.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin hukumar da lamarin ya shafa don jin me ya kawo dogayen layuka a gidajen mai, amma lamarin ya faskara.