Farashin litar man fetur ya yi tashin gwauron zabo zuwa Naira 1,200 a gidajen mai a a Jihar Kano.
Gidajen mai masu zaman kansu sun kara farashin ne a safiyar Talata.
Sun dauki matakin ne a daidai lokacin da gidajen man. NNPCL suka ƙara nasu farashin zuwa N904 a jihar.
A halin da ake ciki dai masu ababen hawa sun yi dogayen layi a gidajen man NNPCL da ke Kano domin shan mai.
Wani jami’i a wani gidan man NNPCL da ke Kano ya shida wa Aminiya cewa suna jiran a ba su umarnin sayar da man a akan sabon farashi.
“Kawai zuwa muka yi aiki muka ga an canza farashi kamar yadda kake gani. Yanzu umarni kawai muke jira.
Wani wanda ya je shan mai ya ce, “mun shiga uku a ƙasar nan, ima muka dosa? Wannan babban abin takaici ne.
Shi kuma Ibrahim Saleh ya bayyana yadda ba ya ba a matsalar mai amma yanzu fetur na kamshin turaren dan goma a Najeriya..
“Na tuna lokacin da aka taba rage farashin lurar fetur a lokacin mulkin Yar’Adua zuwa N65, na zan taba manta wannan abu ba.
“Amma yanzu duk farashin abin da aka kara a ƙasar nan ba ya raguwa.”