Matatar Mai ta Ɗangote ta rage farashin litar man fetur zuwa Naira 865 ga dillalai masu saya daga wurinta bayan an ci gaba da tsarin sayar wa matatun cikin gida a Najeriya ɗanyen mai a farashin naira.
A safiyar Alhamis hukumomin Matatar Ɗangote suka sanar da dillalai dangane da ragin naira 15 daga tsohon farashin man na naira 880.
Tun da farko wasu dillalai sun bayyana cewa akwai yiwuwar matatar ta rage farashin fetur wanda zai kawo sauƙinsa a ƙasa.
Sakataren Ƙungiyar Manyan Dillalan Man Fetur, Chinese Ukadike, ya bayyana tabbacin samun raguwar farashin a Najeriya sakamakon umarnin gwamnati na fara sayar da ɗanyen mai da farashin Nnaira ga matatun cikin gida.
- Tarkon Mutuwa a Katsina: Hanyar Funtua zuwa Ƙanƙara
- Mutanen da suka saba ba ni abinci yanzu na neman taimako — Obi
A ranar Laraba ne Majalisar Zartaswa ta Kasa ta ba da umarnin cikakken aiwatar da tsarin sayar da ɗanyen man da farashin naira da aka dakatar.
Ana iya tuna cewa dakatarwar da Kamfanin Mai na Kasar (NNPC) ya yi bayan ƙarewar wa’adin yarjejeniyar ya haddasa tashin farashin fetur a matatar Ɗangote da ma gidajen man NNPC da na ’yan kasuwa a Najeriya.
Lamarin ya sa matatar ta Ɗangote da sauran ’yan kasuwa daga kara a yayin da ta koma shigowa da ɗanyen mai daga ƙasashen waje.