✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wa ya ba da umarnin kara kudin man fetur?

Gidajen man NNPCL da masu zaman kansu sun kara farashi, amma kamfanin ya ce ba da umarninsu aka yi karin ba.

Masu amfani da man fetur a Najeriya sun shiga rudani bayan gidajen man kamfanin mai na kasa (NNPCL) sun kara kuɗin lita.

An wayi garin Talata gidajen man kamfanin sun kara farashin litar fetur zuwa N955 a wasu wuraren kuma N904.

Gidajen mai masu zaman kansu kuma sun kara nasu farashin zuwa N1,200, da cewa sun samu sanarwar umarnin karin farashin daga NNPCL.

Sai dai kuma daga bisani kamfanin ya lashe amansa, inda hukumar gudanarwarsa ke cewa ba kara farashi ba ta da masaniyar karin da gidajen man nasa suka yi.

Wasu kafofi dai sun yi ta riya cewa Ma’aikatar Man Fetur wadda Shugaba Bola Tinubu da Ƙaranin Ministan Man Fetur, Heineken Lokpobiri suke jagoranta ce ta bayar da umarnin ƙari farashin.

Sai dai kuma a safiyar Gwamnatin Tarayya ta musanta kanta da karin farashin da gidajen man NNPCL suka yi, tana mai cewa babu ruwan ma’aiakatar da sanya farashi, ballantana ta umarci NNPCL ya kara ko a rage.

Lokpobiri ta hannun hadimarsa, Nnemaka Obi,  ya ce babu kamshin gaskiya a cikin lamarin.

Daga bisani kuma, hukumar gudanarwar Kamfanin NNPCL, wanda mallaki Gwamnatin Tarayya ne, a cikin wani sako ya nesanta kansa da ba da umarni ga gidajen mai su kara farashin.

Wannan lamari dai ya haifar da rudani ga masu ababen hawa da sauran masu amfanin da mai, inda tuni jama’a suka fara yin dogayen layika a gidajen man NNPCL domin su samu da suaki.

Masu harkar bumburutu dai tuni suka wasa wukarsu, inda suka fara cin kasuwa a sakamakon wannan hali da aka shiga.

Wannan dambarwa na zuwa ne a ranar da katafariyar Matatar Man Dangote mai karfin samar da tataccen mai lita 650,000 a kullum ta fara aiki.

Hukumar Kasuwacin Mai ta Kasa (NMDPRA) ta ce matatar ta Dangote za ta fara samar da lita milian 25 na fetur kullum a cikin gida a watan nan na Satumba, 2024.

Zuwa watan Oktoba kuma ana sa ran matatar za ta kara adadin tataccen man da take samarwa a cikin gida zuwa lita miliyan 30, a cewar NMDPRA