Dogaen layukan ababen hawa sun dawo a gidajen mai a Abuja bayan wasu daga cikin gidajen sun kara farashin lia daga N617 zuwa N640.
Binciken Aminiya ya gano duk da karin N23 da gidajen mai masu saman suka yi a kan lita, wasu gidajen man, musamman na NNPC ba su kafara farashi ba.
Doga layukan sun kawo cunkosun ababen hawa a kan titunan garin Abuja, musamman a gidajen man NNPC biyu da ke kan titin Olusegun Obasanjo a unguwar Wuse 2.
Gidan man Total Energies’ da ke Wuse Zone 6 kuma rufe shi aka yi, duk da cewa na Wuse Zone 2 yana bude kuma akwai dogon layi, haka ma a gidajen man NNPC da ke unguwar.
A gidan man Mobil da ke Utako ma an samu dogon layin ababen hawa da ke saya a kan N640; gidan man ETERNA da ke unguwar Jabi kuma ba ya aiki.
An samu dogon layi a gidajen BOVAS, Salbas, Shema da AA Rano da ke kan titin Airport.
Kan famfo daya dag cikin 30 da ke gidan AA Rano a Jabi kadai ke ba da mai, kuma kuma ababen hawa kadan ake bari su shiga gidan man a lokacin hada wannan rahoton.
Wani direban tasi, Salisu Ibrahim, ya shaida wa wakilinmu cewa tun ranar Juma’a aka fara samun layi inda wasu gidajen mai ke sayar da lita a kan N630 wasu kuma N640.
Ya ce “Tun ranar Juma’a wasu gidajen man suka fara rufewa, ana rade-radin za su kara kudin lita zuwa N700.”
A watan Oktoba, Shugaban Hukumar NMDPRA mai kula da albartun mai, Farouk Ahmed, ya sanar cewa NNPC na da man da zai wadaci Najeriya.
Amma ya shaida wa wani taron masu ruwa da tsaki cewa ’yan kasuwar da gwamnati ta ba wa lasisin shigo da tataccen man suna korafin rashin samun Dala a kan farashin gwamnati, wanda hakan ya sa kudin da suke kashewa na shigo da man yake karuwa.
Ya ce sun bayyana cewa ba za su ci riba ba idan suka sayar a kan farashin man na yanzu kuma ba za su iya gogayya da NNPC ba da ke shigo da man a kan farashin Dala da gwamnati ta kayyade.