✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun kashe kwamandan jami’an tsaro a Katsina

’Yan ta’addan sun gamu da tirjiyar jami’an tsaro da aka yi karon batta a tsakanin bangarorin biyu.

A daren jiya Lahadi ne wata tawagar ’yan fashin daji ta kai wani mummunan hari a garin Zakka da ke Karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan ta’addan sun kai harin ne da nufin kara nunawa tare da fadada munanan ayyukansu na ta’addanci.

Sai dai wannan hari ya gamu da cikas ta dalilin fitar jami’an tsaron da suka hada da sojojin sama da ’yan sanda tare da jami’an tsaron al’umma da ake kira da “Community Watch Corps”.

’Yan ta’addan sun gamu da tirjiyar jami’an tsaro da aka yi karon batta a tsakanin bangarorin biyu, wanda a dalilin haka kwamandan wannan jami’an tsaron na al’umma mai suna Mujitaba Salisu da wani dan sandan kwantar da tarzoma guda suka riga mu gidan gaskiya.

Kazalika, an yi wa ’yan daban dajin mummunar barna, inda suka kwashe gawarwakin su suka koma daji kamar yadda suka saba.

Ana iya tuna cewa, a ’yan kwanakin nan wasu iyalai suka yi koken cewa wadannan jami’an tsaron al’ummar sun kashe wani dan uwansu da wasu mutane biyu a garin na Zakka.

Ita dai Karamar Hukumar Safana na daya daga cikin kananan hukumomin da ayyukan ’yan daban dajin suka yi kamari.