✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwadago sun tsunduma yajin aiki

Yajin aikin zai ci gaba da gudana har sai gwamnatoci a dukkan matakai sun sauke nauyin da rataya a wuyansu.

Gamayyar kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun sanar da tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga karfe 12:00 na daren wannan Litinin wayerwar garin Talata.

A wannan Litinin din ce dai Ƙungiyar Ƙwadagon ta umurci mambobinta da su fara yajin aikin gama-gari a fadin kasar sakamakon harin da aka kai wa shugaban NLC, Joe Ajaero.

Wata sanarwa da NLC da takwararta ta TUC suka fitar, ta ce an bai wa dukkan rassanta da kuma mambobi ke faɗin jihohi umarnin shiga yajin aikin.

Shugaban TUC, Festus Osifo, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a hedikwatar ’yan kwadagon, ya ce yajin aikin zai ci gaba da kasancewa har sai “gwamnatoci a dukkan matakai sun farga da alhakin da ya rataya a wuyansu.”

Karin bayani na tafe…