Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), ya ɗora alhakin ƙarancin man fetur da ake fama da shi a ƙasar a kan ambaliyar ruwa da kuma rashin kyawun yanayi.
Kusan mako guda kenan da aka fara samun dogayen layuka a gidajen mai a faɗin ƙasar nan, wanda hakan ya sa wasu gidajen man ƙara farashin man da suke siyarwa kan kowa lita.
- El-Rufai da Majalisar Kaduna: Kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 17 ga Yuli
- Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin shinkafa da wasu kayan abinci
Wata sanarwa da NNPCL ya fitar ta ce “Hakan ya faru ne sakamakon matsalar jigilar sauke man daga manya zuwa ƙananan jiragen ruwa na dako.
“Haka nan, saboda hatsarin da ke tattare da fetur da kuma bin umarnin hukumar kula da yanayi cewa kada a yi jigilar mai yayin da ake tsaka da kwarara ruwan sama da tsawa, ba zai yiwu a yi lodin mai ana tsaka da tsawa da walkiya da kuma shatata ruwa ba.
“Hakan nan, matsalar ta ƙaru ne saboda ambaliya ta mamaye wasu hanyoyin manyan motoci, abin da ya kawo tsaiko a jigilar man daga tashohin ruwa zuwa Abuja.”
Samun dogayen layuka a gidajen sayar da man fetur ba sabon abu ba ne a Najeriya, ko a watannin baya an samu irin hakan, inda wasu gidajen man suka dinga sayar da man a kan farashin da ya haura Naira 1000 kan kowa lita.