✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

WAEC ta kara kudin jarrabawa daga N13,950 zuwa N18,000

WAEC ta ce tsada da kuma hauhawar farashin kayayyaki ce ta janyo karin.

Hukumar WAEC mai shirya jarrabawar kammala karatun sakandire a Yammacin Afirka, ta sanar da kara naira 4,050 a kudin jarrabawar kan kowane dalibi.

Hukumar ta ce a yanzu duk dalibin da zai yi rajistar zana jarrabawar a badi sai ya biya Naira 18,000 maimakon Naira 13,950 da aka saba biya a shekarun baya.

Abin da sakin Nnamdi Kanu zai haifar a Najeriya — CNG ta gargadi Buhari

Shugaban Hukumar WAEC a Najeriya, Patrick Areghan ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a ofishinsu da ke Jihar Legas yayin sanar da cewa hukumar ta saki sakamakon jarrabawar dalibai ta 2021.

Sai dai Mista Areghan ya alakanta karin kudin jarrabawar da yadda tattalin arzikin kasar nan ya kasance la’akari da tsada da kuma hauhawar farashin kayayyaki wanda ya ce annobar Coronavirus ce ta haddasa.

WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2021

A ranar Litinin ce Hukumar WAEC) ta saki sakamakon jarabawar kammala sakandire ta shekarar 2021 kamar yadda Mista Patrick Areghan ya tabbatar.

A cewarsa, jimlar dalibai 1,573,849 ne suka yi rajistar jarabawar a cibiyoyi 19,425 da hukumar ta amince da su a fadin kasar nan, inda daga ciki kuma 1,560,261 suka zana jarabawar a bana.

Sanarwar ta ce akalla dalibai 1,274,784 ne suka sami nasara a darusa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.

Ya kuma ce hukumar ta rike sakamakon dalibai kimanin 170,146 da ta samu da laifukan satar jarabawa.

Kazalika, sanarwar ta ce tuni hukumar ta fitar da sakamakon dalibai 1,256,990, kimanin kaso 80.56 cikin 100 na daliban da suka zana jarabawar a Najeriya a bana.

Patrick ya kuma ce suna nan suna kokarin fitar da sakamakon ragowar daliban, wadanda ya ce wasu matsalolin da suka samu da wasu daga cikin darusan da suka zana ne suka haifar musu da tsaikon.

Hukumar dai ta ce lambobin sirrin da za a yi amfani da su wajen duba sakamakon jarabawar na nan a jikin katin da suka yi amfani da shi wajen rubuta jarabawar.

Sanarwar ta kuma ce jarabawar, wacce aka shafe sati bakwai ana yi a bana dai ta yi fama da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na kasar nan.