Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa.
Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya.
Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini.
Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki.
Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da agazawa a fannin ilimi inda ya bukaci daliban da suka amfana da su tabbatar sun yi amfani da damar yadda ya dace, kana su mayar da hankalinsu ga karatunsu da sauran harkokin rayuwarsu na yau da kullum.
A jawabinsa Shugaban Kwamitin Jarabawar ta WAEC, Malam Awaje Nasarawa da Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Keffi, Honorabul Damagani da sauran manyan baki, sun yaba wa dan majalisar, sannan suka bukaci daliban da su yi kyakkyawar amfani da damar don kyautata rayuwarsu a nan gaba.
Wasu daga cikin daliban da suka amfana sun yaba wa dan majalisar inda suka yi addu’ar Allah Ya saka masa da alheri.