Mutanen da suka yi garkuwa da dan Hakimin garin Zip da ke Jihar Taraba, Alhaji Uba, tare da wasu mutum shida, sun bukaci a basu Naira miliyan 120 kafin su saki mutanen.
Sai dai basaraken ya ce basu da kudin ba za su biya.
- PDP za ta kalubalanci tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara a kotu
- Abin da fim din Sanda zango na biyu ya kunsa —Abale
Hakimin ya shaida wa wakilin Aminiya cewa masu garkuwar sun kama dan nasa mai suna Buhari tare da mutane shidan a garin Illela da ke Karamar Hukumar Karim Lamido mako biyu da suka wuce.
Ya ce masu garkuwa da mutanen sun nemi a biya kudi Naira miliyan 30 a kan kowane daya cikin mutanen bakwai kafin su sakesu.
Alhaji Uba ya ce duk lokacin da masu garkuwar suka kira shi sai sun zage shi saboda kawai ya ce basu da wadannan kudin.
Hakimin ya shaida wa wakilin namu cewa wasu daga cikin iyaye da ’yan uwan wadanda aka yi garkuwar da su basu da ko N10,000.
Ya ce shi kan shi a matsayin Hakimin garin bai taba rike miliyan daya ba, balle miliyan 30.
Ya ce al’ummar masarautarsa na cikin mawuyacin hali saboda matsalar ’yan ta’adda wadanda y ace sun mamaye yankin nasa.
Kakakin Rundunan ’Yan Sanda na Jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin.