Kwana uku da sace ma’aikata sama da 40 ciki har da yara 39 a wata gona da ke unguwar Mai Ruwa a Karamar Hukumar Faskarin Jihar Katsina, masu garkuwa da su na neman Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansa.
Sun kuma ce suna son tattaunawa da mai gonar da aka yi garkuwa da mutanen a ciki.
Maharan sun kuma sha alwashin cewa ba za su saki mutanen da suka sace ba har sai an biya musu bukatunsu.
Wadanda abin ya shafa sun fito ne daga kauyuka daban-daban a Kananan Hukumomin Faskari da Funtuwa da ke Jihar ta Katsina.
Wata majiya a yankin ta ce ’yan bindigar sun mamaye gonar ce da yammacin Lahadi, inda suka tafi da ma’aikata sama da 40 da ke aiki a gonar.
Adadin ya hada da yara 39 da suka gaza tserewa yayin da ’yan bindigar suka kai harin.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda dalilai na tsaro ta ce maharan sun tuntubi wasu daga cikin iyayen yaran da suka sace a ranar Litinin, inda suka bukaci miliyan 30 kafin su sako su.
“Mai gonar ba ya kusa. Ita [gonar] tana karkashin daya daga cikin ma’aikatansa. A lokacin da aka yi garkuwa da wadanda abin ya shafa, sai (’yan bindigar) suka tuntubi iyayen yaran tare da bukatar kudin fansa amma sun ce ba za su karbi kasa da abin da suka bukata ba ko kuma kai tsaye a hada su da mai gonar.
“Sun ce sun yi bincike kuma sun gano cewa mai gonar yana da arziki sosai. A halin da ake ciki yanzu sun dage sai sun yin magana da mai gonar,” inji shi.
Sai dai ya kasa tabbatar da ko mai gonar ya amince ya yi magana da masu garkuwar.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isa, ya ce rundunar tana sane da faruwar lamarin.
Gambo, ya ce dakarunsu na kan kokarin ceto wadanda aka sace, kodayake bai bayyana adadin wadanda aka sace yayin harin ba.
“Eh, mun samu rahoton kuma muna aiki don ceto su. Zan nemi cikakken bayani game da sace mutanen kamar yadda DPO ya aike min sannan zan sanar da ku me ake ciki,” in ji shi.
Al’ummar jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Zamfara, Katsina, Kaduna, Sakkwato, Kebbi da kuma Neja a arewa ta tsakiya sun shafe shekaru suna fama da hare-haren ta’addanci.
’Yan ta’addan dai sun dade suna takura wa mazauna yankin, musamman manoma.
Wani bincike ya gano yadda ’yan ta’adda ke sanya manoma barin gonakinsu ko kuma tilasta musu biyan harajin noma domin shiga gonakinsu.