✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Uwa ta sa danta ya kashe baffansa

Ana zargin wata matar aure ta sanya danta ya kashe kanin mahaifinsa kuma jagoran neman auren ’yarta.

Ana zargin wata matar aure ta sanya danta ya kashe kanin mahaifinsa kuma jagoran neman auren ’yarta.

Ana zargin matar ta sanya dan nata mai shekaru 23 ya kashe kanin mijinta kuma kaninta na dangi mai suna Abubakar Adamu Biso mai shekaru 26, saboda sabanin da suka samu kan kudin toshin ’yarta.

Marigayin ya gamu da ajalinsa ne bayan dan yayarsa ya sossoka masa wuka a unguwar Zangon Shanu, Samaru da ke Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna.

Yayan marigayin mai suna Ibrahim Adamu Biso, ya yi wa Aminiya karin bayanin cewa, “Rashin jituwar ya samo asali ne a kan kin yardar ita matar yayan marigayin a cika alkawarin da aka yi wa abokin marigayin, na aura masa ’yarsu wadda shi marigayin ya yi wa abokin nasa hanyar neman auran ’yar yayan namu, inda ita kuma matarsa daga baya ta ki amincewa.

“Don haka sai shi marigayin ya ce tunda haka ya faru to sai a maido wa da abokin nasa da duk abubuwan da aka san ya bai wa budurwar, tunda ba za a ba shi aurenta ba.

“Wannan shi ne ya haifar da rashin jituwa tsakaninsu har da bakaken maganganu, bayan an shiga tsakani, sai ita ta ce wa marigayi wallahi ita ba za ta yarda ba, kuma yasan halin ’ya’yanta don haka za ta sa su daukar mata fansa.”

Ibrahim Biso, yayan marigayin, ya kara da cewa, “Ko minti 20 ba a yi ba da shi marigayi ya dawo shago wajen sana’arsa, sai ga daya daga cikin su (yaran) dauke da sharbebiyar wuka a hannu ya fada shagon marigayin, kafin a farga, ya sossoka mishi wukar nan ta wuyansa da sauraran bangarorin jikinsa.

“Da jin ihu sai nan da nan muka kutsa shagon tunda dama wurin muke kasuwancinmu gaba dayanmu, muka ga abin da ya faru, to sai mukayi kokarin kama shi muka kwace wukar.

“Sannan muka dauki marigayi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, india a nan ne Allah Ya karbi rayuwarsa, sakamakon raunukar sukar wukar da yaron ya yi mishi.”

Ya kara da cewa, “Sai dai ita, ganin irin barnar da shi dan nata ya yi, da kuma yadda al’ummar anguwar suka taso, sai ta gudu, har yau ba a san inda take ba.

“Amma shi wanda ya aikata kisan yana han hannun ’yan sanda a Kaduna, bayan kama shi da al’ummar unguwar suka yi, suka mika wa ’yan sanda yankin Samaru.”

Al’ummar anguwar sun bayyana cewa auren zumunci aka kulla tsakanin mahaifin yaron da mahaifiyarsa, don haka, dan wa ne ya kashe kanin mahaifinsa, kuma kanin mahafiyarsa.

Sun danganta abin da ya faru da rashin tarbiyyada sakacin mahaifin yaron, wanda suka ce ba shi da ta cewa akan yaransa, sai abin da matar ta ce, don haka yaran suke aikata abin da suke so na rashin kyautatawa.

Al’ummar yankin sun yi kira ga hukuma cewa irin wannan kisan kai kusan shi ne na biyar a yankin kuma wasu daga cikin irin wadannan yaran wasu an sako su sun dawo suna yawo, dan sai suka dauki yin hakan ba komai ba.

Sai dai bayan kammala jana’iza washe gari su ’yan sanda yankin Samaru sun tura wanda ake zargin zuwa babban ofishinsu da ke Kaduna.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sanda Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, amma hakan bai samu ba.

Mun fara magana da shi, sai wayar ta katseh, daga baya ya ce zai kira daga baya, domin kwamishina na neman sa a lokacin.

Amma kuma, har muka gama hada wannan labarin ba mu samu ji daga gare shi ba.