✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Uwa ta haka rami mai nisan kafa 35 don kubutar da danta daga kurkuku

An kama wata mata mai shekara 51 ’yar kasar Ukraine bayan da aka gano ta haka rami mai zurfi a karkashin kasa kusa da katangar…

An kama wata mata mai shekara 51 ’yar kasar Ukraine bayan da aka gano ta haka rami mai zurfi a karkashin kasa kusa da katangar gidan yari, da nufin kubutar da danta da ke tsare a cikin kurkukun.

Matar wadda aka sakaya sunanta ta fito ne daga yankin Nikolaeb da ke Ukraine, kuma ana zargin ta kama hayar wani gida da ke makwabtaka da kurkukun da ake tsare da danta bayan kama shi kan zargin kisan kai.

Ana zargin kullum cikin dare takan je da fitila kusa da kurkukun birnin Zaporizhia da ke da wadatattun jami’an tsaro, ta tafi da abin hakar rami ta haka kamar kafa 10 kusa da iyakar gidan yarin.

Matar dai tana aikin ne kawai da daddare tana amfani da abin daukar kaya tana dibe kasar ramin da ta hako da abubuwan da ta fitar daga cikin ramin.

Ana kuma zargin ta kai kimanin mako uku tana haka ramin inda ta kai ga cimma katangar kurkukun kafin a kama ta.

Mahaifiyar wannan fursuna tana zaune ne a cikin gidan da take haya da rana kadai, da daddare sai ta fice, saboda kada makwabta su fahimci inda take zuwa.

Kuma ta yi nasarar bin wannan tsari da ta daukar wa kanta, kuma a lokacin da aka kama ta makwabtanta ba su iya gane ta ba.

Wata kafar labarai ta kasar Ukraine ta wallafa cewa a lokacin da aka kama matar ta riga ta haka rami mai zurfin kafa 35, inda ’yan sandan da suka kama ta su kansu sun jinjina mata kan aikin da ta yi. A cikin mako uku ta fitar da kimanin kasa tan uku daga cikin ramin.

Wasu rahotanni sun ce matar ta fara haka ramin ne daga cikin gidan da take, kuma ta amsa laifin hakar ramin don kubutar da danta.

A yanzu dai tana hannun jami’an tsaro, sai dai duk da laifin da ta yi, wadansu mutanen kasar suna jinjina mata kan kokarin da ta yi na hakar rami don ceto danta.

Wannan uwa ta shirya tsaf don kubutar da danta. Sai dai a wani rahoto an ce mahaifinta mai hakar ma’adanai ne, kuma ya ce ko hakar ramin da ya kai mita uku ba karamin aiki ba ne.

Wani makwabcin matar mai suna Serhey Pilnyansky ya bayyana wa manema labarai matar ba ta da wani abin hakar rami, amma ta yi wannan kokarin.

Wani mai yin sharhi dan asalin garin, cewa ya yi wannan uwa ce tagari, ba wanda ta yasar da danta ba.