Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16.
Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano.
- Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa
- HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano
Barau ya gana da iyalan mamatan a Masallacin At-Taqwa da ke Bunkure a ranar Laraba tare da Ministan Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da sauran manyan jami’ai.
Barau, ya yi ta’aziyya da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci.
“Na zo nan ne domin na taya ku jaje kan wannan mummunan al’amari da ya jawo rasuwar ’yan uwanku 16 a ranar Alhamis da ta gabata.
“Allah Ya Aljanna Firdausi ta zama makomarsu, Ya bai wa waɗanda suka ji rauni lafiya,” in ji Barau.
“Ba za mu ɗauki hakan da sauƙi ba. Za mu tabbatar cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci.”
Barau, ya kuma sanar da bai wa kowane daga cikin iyalan mamatan kyautar Naira miliyan ɗaya, wanda ya kai jimillar Naira miliyan 16.
Da yake magana a madadin iyalan mamatan, Sheikh Zainul Abidina Auwal, limamin yankin, ya gode wa Barau bisa ƙoƙarinsa da yadda ya damu da lamarin.