Manchester United ta lallasa takwararta Manchester City da ci 2-1 a wasan hammayya da kungiyoyin biyu suka kece raini a filin wasa na Old Trafford.
City ce ta fara cin kwallo ta hannun Jack Grealish a kokarin da kungiyar ke yi na rage yawan tazarar maki da ke tsakaninta da Arsenal wadda ke ta daya a kan teburin Firimiyar Ingila.
- Idanun ’yan siyasa sukan rufe da zarar sun samu mulki —Jonathan
- Qatar na shirin sayen kungiyoyin Firimiyar Ingila uku
To sai dai hakar City ba ta cimma ruwa ba, bayan da Bruno Fernandes ya farke kwallon ana saura minti 12 a tashi wasan, duk da kasancewar Marcus Rashford a cikin da’irar satar gida.
Minti hudu bayan hakan ne kuma Marcus Rashford din ya kara ta biyu bayan da ya zura kwallon da Alejandro Garnacho ya bugo masa daga kusa da kusurwa.
Da wannan sakamako United ta koma ta uku a kan teburin, maki daya tsakaninta da City wadda ke matsayi na biyu, sannan kuma maki biyar tsakaninta da Arsenal ta daya.