✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

United ta kwashi kashinta a hannu a Etihad

United ta yi rashin nasara karo na 18 a Firimiyar Ingila a hannun City.

Ƙungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United ta kwashi kashinta a hannu yayin da ta je bakunta filin wasa na Etihad a wannan Lahadin. 

Manchester City dai ba sani ba sabo ta nuna yayin da ta kwarara wa United kwallaye 6-3 a wasan makon na takwas a gasar Firimiyar Ingila.

Tun kan a tafi hutun rabin lokaci dai City ta ci kwallo 4-0 ta hannun Phil Foden da Erling Haaland kowanne ya ci bibiyu.

Bayan da suka huta suka koma karawar zagaye na biyu Foden da Haaland kowanne ya kara zura kwallo a raga.

Sai dai United ta zare uku ta hannun Dos Santos, sannan Anthony Martial ya zura biyu a raga, daya daga ciki a bugun fenariti a mintin karshe.

Da wannan sakamakon City ta ci gaba da zama a mataki na biyu a kan teburin Firimiyar da maki 20.

Ita kuwa United tana nan da makinta 12 tana kuma ta shida a teburin wasannin bana.

Manchester City ta yi nasara karo uku a jere a kan United tun bayan doke ta hudu da ta yi tsakanin Afirilun 2013 zuwa Nuwambar 2014.

Kamar yadda alkaluma na tarihi suka nuna, United ta yi rashin nasara karo na 18 a Firimiyar Ingila a hannun City.

%d bloggers like this: