Rahotannin da ke fitowa daga Ingila suna nuna kulob din Manchester United da na Leicester City suna rububi wajen ganin sun dauke dan kwallon Najeriya Ahmed Musa da yanzu haka yake kwallo a kulob din CSKA Moscow da ke Rasha.
A tayin farko da Leicester ta yi a kan Ahmed Musa na Dala miliyan 21.6 CSKA Moscow ta ki amincewa inda ta dage lallai sai an lale mata Dala miliyan 27 kwatankwacin Naira biliyan 8 da miliyan 154 kafin ta rabu da shi. Hakan ta sa kulob din Leicester ya zage damtse wajen ganin ya biya kudin da ake bukata kafin a rufe kasuwar cinikin ‘yan kwallo a makon gobe.
Haka ma kulob din United, an ruwaito Koci Louis ban Gaal ya fara tunanin dauke dan kwallon kafin a rufe kasuwar cinikin ‘yan kwallo a ranar 1 ga watan gobe. Rahotanni sun nuna tuni mahukunta kulob din United suka fara tunanin hanyoyin da za a bi wajen cefano dan kwallon kafin a rufe kasuwar cinikin ‘yan kwallo.
Rahoton ya ce kulob din CSKA Mosko tuni ya sanya masa farashin Fam miliyan 18.9 kwatankwacin Naira Biliyan takwas da miliyan 154 a matsayin kudin da zai sayar da shi ga duk kulob din da ke bukatarsa. Hakan ta sa kulob din Leicester City ya shiga nazarin hanyoyin da zai bi don ganin an samu daidaiton farashi a kan dan kwallon kafin a rufe kasuwar cinikin ’yan kwallo a makon gobe.
Idan cinikin ya kullu, ana sa ran Ahmed Musa zai buga wasan da kulob din Leicester zai yi da na Liberpool a gasar rukunin firimiya na Ingila a ranar Talata mai zuwa.
Kulob din Leicester City ne yake saman tebur a gasar rukunin firimiya a halin yanzu da maki 47 sai kulob din Manchester City ke biye da maki 44 yayin da Arsenal ke matsayi na uku da maki 44 sai Tottenham ta kasance ta hudu da maki 42.
United da Leicester City suna zawarcin Ahmed Musa
Rahotannin da ke fitowa daga Ingila suna nuna kulob din Manchester United da na Leicester City suna rububi wajen ganin sun dauke dan kwallon Najeriya…