Yankunan karkarar Jihar Yobe za su ci gajiyar rijyoyin burtsatse 488 don samun ruwan sha da kayayyakin tsabtace shi nan ba da dadewa ba. A ranar 22 ga Janairu ne Alhaji Mohammed Bukar, Manajan Hukumar Samar da Ruwa a Yankunan Karkara ta Jihar Yobe (RUWASSA) ya ce aikin ya hada da famfunan tuka-tuka 380, da rijiyoyin burtsatse masu aiki da hasken rana 48 da kayayyakin tsabta guda 60 a makarantaun firamare da asibitoci. Alhaji Zarma Abatcha, Shugaban karamar Hukumar Dapchi cewa ya yi, aikin za a aiwatar da shi a karkashin yarjejeniyar hadin gwiwa ta bangarorin uku da aka kulla a tsakanin Asusun Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) da Gwamnatin Yobe da karamar Hukumar Busari. UNICEF za ta zuba kudin da suka kai Naira miliyan 649.6, sai Gwamnatin Yobe Naira miliyan 263 da dubu 800, sannan karamar Hukumar Busari za ta zuba Naira miliyan 111 da dubu 300 a aikin samar da ruwa da kula da tsabta a yankunan,” inji shugaban.
Zanna ya bayar da tabbacin tsayuwar jihar da karamar hukumar don bayar da kasonsu, ta yadda za a samu nasarar aiwatar da ayyukan. Mai magana da yawun al’ummomin da za su ci gajiyar ayyukan, Malam Modu Masaba, ya yaba wa gwamnatin Yobe kan fito da da wannan tsari, sannan ya yi kira ga gwamnatin jihar da karamar hukumar su yi kokrin biyan nasu kason kudin a kan kari, ta yadda Asusun UNICEF zai bayar da nasa kason. Ya ce gina rijiyoyin burtsatsen don samar da ruwa zai kawo karshen matsanaciyar wahalar ruwa da ke ci wa al’ummomin yankin tuwo a kwarya, tare da magance cututtuka masu yaduwa da ake samu daga gurbataccen ruwa. “Idan aka samar da rijijiyoyin, kashi 70 cikin 100 na matsalolin lafiya da suka addabi al’ummomin yankunan karkara za a shawo kansu,” inji Masaba.