✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Umarnin kotu ba zai hana mu gudanar da tarukan ranar Asabar ba – APC

APC ta kuma ce za ta hukunta wadanda suka shigar da karar.

Jam’iyyar APC mai mulki ta ce tarukan da ta shirya gudanarwa a matakan Kananan Hukumomi ranar Asabar na nan daram, duk kuwa da umarnin kotun da ya hana ta yin hakan.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai wata Babbar Kotu a birnin Asaba na Jihar Delta ta yanke wani kwarya-kwaryar hukunci da ya dakatar da APC daga shirya tarukan.

Kazalika, kotun ta kuma umarci shugabancin jam’iyyar karkashin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni da sauran ’yan kwamitinsa da su daina gabatar da kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar.

To sai dai Sakataren riko na jam’iyyar, Sanata John James Akpanudoedehe ranar Alhamis a Abuja ya kaddamar da kwamitin da zai shirya taron, inda ya ce jam’iyyar za kuma ta hukunta wadanda suka kai ta karar.

“Kamar yadda a ko da yaushe Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke ba jakadunsa shawara, muna kira gareku da ku je ku tunkari aikin da ke gabanku ba tare da duk wata fargaba ba.

“Muna kuma amfani da wannan damar wajen jaddada matsayin Kwamitin Zartarwar Jam’iyyarmu na kasa cewa za a dauki tsattsauran hukunci a kan wadanda suka gurfanar da jam’iyya a gaban kotu,” inji shi.

Shi kuwa Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar na kasa, Yekini Nabena ya shaida wa wakilinmu cewa hukuncin kotun ta Asaba ba ta inda zai shafi ayyukan kwamitinsu, inda ya ce sai da suka gudanar da zuzzurfar tattaunawa kafin su yanke hukuncin ci gaba da shirya taron na ranar Asabar.

Tun da farko dai Sanata Akpanudoedehe a cikin wata sanarwa ya ce shugabancin jam’iyyar na kasa ya kori shugaban jam’iyyar a Karamar Hukumar Yola ta Kudu da ke Jihar Adamawa, Alhaji Sulaiman Adamu, saboda zagin Shugaba Buhari.