Gwamnatin Ukraine ta yi ikirarin kakkaɓo jirage marasa matuƙa guda 27 daga suka kawo mata hari daga Rasha, a safiyar Alhamis.
Rundunar Sojin Sama ta Ukraine ta ce na’urarar tsaron sararin samaniyar ƙasarta ne suka harbo jiragen, samfurin Shahed a cikin dare.
- NAJERIYA A YAU: Shin Matasa Sun Gamsu Da Ministocin Da Ake Son Naɗa Musu?
- Dubban mutane sun tsere bayan hari a kauyuka 7 a Kebbi
“Jirage marasa matuƙa guda 30 ne suka kawo mana hari… kuma mun kakkaɓo guda 27 daga cikinsu samfurin Shahed,” in ji rundunar ta shafinta na sada zumunta.
Sai dai sanarwar ba ta ce komai game da ragowar jiragen ko barnar da suka yi ba.
A baya-bayan nan dai manyan abokan gaban (Rasha da Ukraine) sun zafafa kai wa juna hari ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa.
Kowacce daga cikin kasashen masu makwabtaka da juna kan yi ikirarin kakkaɓo jiragen abokiyar gabarta, a yakin da suka shafe watanni suna gwabzawa.