✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uba Sani ya yi jajen ’yan ɗaurin aure 12 da aka kashe a Filato

Kwamishinan 'Yan Sandan jihar ya ce ana bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin.

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan matafiyan da aka kashe a garin Mangu na Jihar Filato, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure.

A yayin isar da saƙon a ƙauyen DanBami da ke Anguwar Rimi, a Ƙaramar Hukumar Kudan, Gwamnan ya roƙi Allah Ya gafarta wa mamatan tare da addu’a ga waɗanda suka ji rauni.

Gwamnan, wanda Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Rabi’u Muhammad, ya wakilta, ya ce gwamnati na ƙoƙarin gano waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki.

Ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tuntuɓar Gwamnan Jihar Filato domin ɗaukar matakan da suka dace.

An tabbatar da cewa mutum 11 daga cikin 31 da ke cikin mota sun rasu, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa bikin ɗaurin auren wani ɗan uwansu a Mangu.

Mutum na 12 shi ne direban motar wanda ɗan asalin garin Basawa ne.

Gwamna Uba Sani, ya ce an kama wasu mutane da ake zargi da hannu a lamarin, kuma gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika.

Ya kuma roƙi al’umma, musamman matasa, da su guji ɗaukar hukunci a hannunsu, domin gwamnati na aiki kafaɗa da kafaɗa da Jihar Filato domin tabbatar da adalci.

“Na jajanta wa iyalan mamatan bisa wannan babban rashi. Ina roƙon ku da ku ɗauki wannan a matsayin ƙaddara. Mutuwa abu ne da babu makawa, kuma kowa zai fuskance ta a lokacin da Allah Ya rubuta masa,” in ji Gwamnan.

A nasa ɓangaren, Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, wanda Hakimin Basawa, Haruna Abubakar, ya wakilta, ya roƙi Allah Ya jiƙan mamatan tare da bai wa iyalansu haƙuri da juriya.

Malam Musa Ibrahim, da ya yi magana a madadin iyalan mamatan da al’ummar DanBami, ya ce sun rungumi ƙaddara bisa wannan al’amari.

Sai dai ya roƙi Gwamnan da ya tallafa wa iyalan ta hanyar biyansu diyya domin rage musu raɗaɗin rashin da suka yi.

Ya ce dukkanin mamatan ‘yan garin ne kuma ‘yan uwan juna ne, direban motar ne kawai daga garin Basawa.