Kasa da sa’o’i 48 da Hadaddiyar Daular Larabawa ta bayar da sanarwar cire takunkumin hana jiragen Najeriya shiga shiga daular, ta sake dakatar da jiragen a ranar Litinin.
“Dangane da umarnin gwamnati, an sake dakatar da zirga-zirgar jiragen fasinja daga Najeriya (Legos da Abuja) wanda zai fara daga 21 ga Yuni 2021 har zuwa wani lokaci,” a cewar wata sanarwar da kamfanin jiragen Emirates ya fitar a shafinsa na intanet a ranar Litinin.
- Saudiyya za ta gina katafariyar makarantar wasanni
- ’Yan bindigar da suka sace ’yan makarantar Yawuri sun fitar da hotunansu
Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Asabar da ta gabata ce Kamfanin Emirates ya sanar da dawo da zirga-zirgar jiragensa da aka dakatar tun a watan Maris na bara bayan bullar cutar COVID-19.
Sanarwar da kamfanin ya fitar na zuwa ne biyo bayan dage takunkumin hana zirga-zirga a kan Najeriya da sauran kasashe da Hadaddiyar Daular Larabawan ta yi.
Kwamitin Yaki da Cututtuka na UAE ya bada umarnin cire takunkumin a kan fasinjojin Najeriya game da cutar Coronavirus, sai dai akwai bukatar yi musu gwajin cutar.
“Mun saukaka wa matafiya shigowa UAE don yi harkokinsu inda za mu ci gaba da jigilar fasinjoji daga Afirka ta Kudu, Najeriya da Indiya bisa wadannan ka’idoji daga ranar 23 ga Yuni,” inji Emirates.
Amma a ranar Laraba ta sake fitar da wata sabuwar sanarwar cewar jiragen da suka taso daga Legas da Abuja ba za su shiga kasar ba.
“Abokan huldarmu da suka taso daga Legas da Abuja, ba za a bari su shiga UEA ba.
“Haka kuma mafiyan da suka taso daga Najeriya tsakanin kwanaki 14 su ma ba za a bari su shiga ba.
“Muna taya abokan huldarmu rashin jin dadin wannan sabon mataki.
“Wadanda suka sayi tikiti za su iya tuntubar kamfanin Emirate don sake neman izinin wani kwanan watan da zarar an sassauta dokar. Muna fatan ci gaba da hulda Najeriya.”