Hadaddiyar Daular Larabawa ta ba wa Najeriya tallafin ton bakwai da rabi na kayan asibiti domin taimakon yaki da cutar coronavirus a Najeriya.
Da yake mika kayan asibitin da na kariyan bayan isowarsu Najeriya, babban jami’in ofishin jakancin UAE a Najeriya, Khalifa Al Mehrezi, ya jaddada goyon bayan kasarsa ga Najeriya a yaki da cutar.
“Matakin kari ne a akan yunkurin UAE na taimaka wa kawayenta yaki da da suke yi da COVID-19, muna kuma tabbatar wa Najeriya cewa za mu ci gaba da hadin gwiwa har mu ga bayan cutar
“Mun yaba da jajircewar Gwamnati da jami’an lafiya da ‘yan jaridar Najeriya da ke aiki wajen shawo kan cutar”, inji a ranar Asabar 15 ga Agusta.
Da take karbar kayan a madadin Gwamnatin Tarayya, Darektar Magunguna da Rigakafi na Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya Misis Olubukola Ajayi, ta yi godiya tare da bayar da tabbatar amfani da su yadda ya dace.