kungiyar kwallon kafa ta kasa ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20) da aka fi sani da Flying Eagles ta lallasa kulob din Katsina United 3-1 a wasan sada zumunta da kungiyoyin biyu suka yi.
kungiyar U-20, wacce Emmanuel Amuneke yake yi wa jagoranci, ta shirya wannan wasa na sada zumunta ne a kokarin tunkarar wasan neman hayewa gasar cin kofin Afirka na matasa da kasar Burundi.
kungiyar za ta hadu da Burundi ne a ranar 22 ga wannan wata a Bujumbura.
’Yan kwallon U-20 Kelechi Nwakali da Udochukwu Ammudu da Kingsley Micheal ne suka zura kwallaye a ragar Katsina United, yayin da ana gab da tashi wasan sai dan kwallon Katsina United Ibrahim Sule ya samu nasarar zura kwallo a ragar Flying Eagles.
Kawo yanzu kungiyar Flying Eagles ta samu nasarar zura kwallaye 20 daga cikin wasanni shida da ta yi a kokarin tunkarar wasanta da Burundi a makon gobe.
U-20 ta lallasa Katsina United ci 3-1
kungiyar kwallon kafa ta kasa ta ’yan kasa da shekara 20 (U-20) da aka fi sani da Flying Eagles ta lallasa kulob din Katsina United…