✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tushen zunubi da hanyar ceto (3)

Barkanmu da sake saduwa cikin nazarinmu a kan tushen zunubi da hanyar samun ceto. A wannan mako za mu ga yadda muka kasa a zamanmu…

Barkanmu da sake saduwa cikin nazarinmu a kan tushen zunubi da hanyar samun ceto.

A wannan mako za mu ga yadda muka kasa a zamanmu na ’yan Adam da kuma yadda Ubangiji cikin jinkanSa Ya nuna mana hanyar kubuta.

Bayan Ubangiji Allah Ya kori Adamu da Hawwa’u daga Gonar Aidan, Littafi Mai tsarki ya nuna mana cewa Hawwa’u ta haifi ’ya’ya maza biyu; Kayinu da Habila Farawa 4:1-5. Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na samu da namiji da iznin Ubangiji.” Ta kuma haifi dan uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne. Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona. Habila kuwa ya kawo nasa kosassu daga cikin ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa Ya kula da Habila da sadakarsa, amma Kayinu da sadakarsa, bai kula da su ba. Saboda haka Kayinu ya fusata kwarai, har ya kwantsare fuskarsa.

Abin da ya faru a nan shi ne Kayinu ya nuna fushinsa, yin fushi kuwa abu ne da Ubangiji Allah ba Ya kaunar Ya ga mun yi wa juna. Alal misali, wani dan uwanka ko a ce wani makwabcinka ya samu karuwa cikin rayuwarsa da dai makamancin haka da Ubangiji ya albarkace shi da shi.

Fushi na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da zunubi. Sanadiyar fusatar da Kayinu ya yi ne har ta kai shi ga zunubin kisa. Galatiyawa 5:19-21 na cewa; “Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato fasikanci da aikin lalata da fajirci da bautar gumaka da sihiri da gaba da jayayya da kishi da fushi da son kai da tsaguwa, da hamayya da hassada da buguwa da shashanci da kuma sauran irinsu. Ina fadakar da ku kamar yadda na fadakar da ku a da, cewa masu yin irin wadannan abubuwa, ba za su samu gado a Mulkin Allah ba.

Abin tambaya a nan shi ne wai shin, zunubi na da sakamako ne a nan gaba? Amsar ita ce kwarai, zunubi na da sakamako, duk wanda rayuwarsa ke cike da abubuwan da muka karanta a cikin Galatiyawa 5:19-21, zai girbi abin da ya shuka da irin wannan halin nan ba da jimawa ba, sakamakon kuwa shi ne hallaka da mutuwa ta har abada. Mutuwa ta har abada kuwa na nufin rabuwa da Ubangiji na har abada. Yakubu 1: 14-15: “Amma kowane mutum yakan jarabtu in mugun burinsa ya rude shi, ya kuma yaudare shi. Mugun buri kuma in ya yi ciki, yakan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, yakan jawo mutuwa.”

Kamar yadda Ubangiji Allah Ya kori Adamu da Hawwa’u hakan nan ma Ubangiji ya yi da Kayinu domin kisan da ya yi ga dan uwansa.

A cikin Littafin Fitowa 20:1-17: Ubangiji Ya bai wa bawanSa Musa dokoki goma don jagora, kuma su zame mana kamar madubi da zai nuna halin mutuntaka da kuma matsayin Ubangiji. Hakkan nan kuma don Ya nuna mana mu masu zunubi ne, mun kuma kasa ga darajar Allah.

A nan mun ga yadda iyayenmu na fari suka kasa ta hanyoyi da dama, haka kuma yake a yau. Mukan saba wa Ubangiji Allah ta hanyoyi daban-daban cikin rayuwarmu ta yau da kullum. Amma da yake Ubangiji Mai jinkai Mai rahama ne, sai Ya kawo mana hanyar ceto ta wurin Yesu Almasihu. Romawa 3:23-26: “Gama ’yan Adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga daukakar Allah. Amma ta wurin alherin da Allah Ya yi musu kyauta, sun samu kubuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi. Allah kuwa Ya ayyana Yesu Almasihu ya zama hadayar sulhu, ta wurin ba da gaskiya ga jininsa. Allah kuwa Ya yi haka domin ya nuna adalcinsa ne, domin saboda hakurinSa Ya jingine zunubban da aka gabatar, domin a nuna adalcinSa a wannan zamani, wato a bayyana Shi kanSa Mai adalci ne, Mai kubutar da duk mai gaskatawa da Yesu kuma.

Manzo Bulus ya sake bayyanawa a cikin wasikarsa zuwa ga masu bin Yesu Almasihu a Roma. Romawa 3:19-20:  “To, mun sani duk abin da Shari’a ta ce, ya shafi wadanda suke karkashinta ne, don a tuke hanzarin kowa, duk duniya kuma ta sani karkashin hukuncin Allah take. Ai, ba wani dan Adam da zai samu kubuta ga Allah ta kiyaye ayyukan Shari’a, tunda yake ta Shari’a ce mutum yake ganin laifinsa. Mun san cewa da ikon kanmu ba za mu iya kubuce wa zunubi ba shi ya sa Ubangiji Allah cikin kaunarSa Ya aiko da Yesu Almasihu don ceton dukkan ’yan Adam.

Amma Ubangiji cikin jinkanSa Ya nuna mana hanyar ceto ta wurin Yesu Almasihu, mai ceton dukkan duniya. Yesu ya zo duniya don fansar mu ’yan Adam ta wurin nuna mana hanyar zuwa wurin Uba. Yahaya 14:6 Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.”

Idan muka bada gaskiya gare shi, muka kuma bi gurbin da ya bar mana, za mu samu ceto da rai madawwami.

Ubangiji Allah Ya kai mu mako mai zuwa lafiya, amin.