✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tushen rikicin Falasdinawa da Yahudawan Isra’ila

Bayan turawa sun zaunar da Yahudawa a yankin kasar Falasɗinu, daga baya Yahudawan suka fara mamaye wasu sassan yankin da cewa kasarsu ce ita asali…

Matsalar Falasdinu da Yahudawan Isra’ila ta faro ne kusan shekara 100 da suka gabata lokacin da Turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka kwace iko da kasar Falasdinu bayan da suka ci Daular Musulunci ta Usmaniyya da yankin Gabas ta Tsakiya ke karkashin ikonta a lokacin Yakin Duniya na Daya.

A lokacin Yahudawa ’yan kadan ne a yankin da Larabawa suke da rinjaye.

Dama Yahudawan sun addabi kasashen Turai wanda shi ne silar Yakin Duniyar.

Hakan ya sa kasashen Turai na Yamma da Gabas suka amince Birtaniya ta kafa kasar da za a kira ta Yahudawa a wurin, wannan shi ne tushen rikicin.

Bayanai sun ce daga farko Turawan sun so su sama wa Yahudawan wurin zama a Afirka ce, amma sai Yahudawan suka ce atafau a Falasdinu za a kafa musu kasa domin nan ne kasar kakanninsu ta asali, yayin da Larabawan Falasdinu suka sa kafa suka shure wannan ikirari suka ki amincewa da shirin kafa kasar Yahudawa a kasarsu.

A tsakanin shekarun 1920 zuwa 1940, yawan Yahudawan da suka koma yankin ya karu, inda yawanci suka rika gujewa daga gallazawar da ake yi musu a Turai bayan kisan-gillar Yahudawa a Yakin Duniya na Biyu.

A 1947, Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar raba Falasdinu gida biyu inda za a kafa kasar Isra’ila da ta Larabawa, yayin da birnin Kudus zai kasance na duniya wato mallakar kasashen biyu.

Shugabannin Yahudawa sun amince da wannan tsari yayin da na Larabawa suka yi watsi da shi, aka kasa aiwatar da shi.

An-Nakba

Da mahukuntar Birtaniya suka kasa shawo kan matsalar a 1948, sai suka fice suka tafi, daga nan sai shugabannin Yahudawa suka yi amfani da wannan dama suka kafa kasar Isra’ila.

Da Falasdinawa suka ki amincewa da hakan sai yaki ya biyo baya.

Sojoji daga kasashen Larabawa masu makwabtaka sun shigar wa ’yan uwansu aka fafata yaki inda kasashen Turai kuma suka goya wa Yahudawan baya, lamarin da ya sa aka tilasta wa dubban Falasdinawa barin gidajensu.

Wannan yaki ne suka sa wa suna An -Nakba.

Ani yi filla-filla da Falasdinu

Zuwa lokacin da aka gama yakin tare da kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta a shekarar, Isra’ila ta riga ta kame mafi yawacin yankin.

Yankin da Jordan ta kama ya zama Gabar Yammacin Kogin Jordan, wanda Masar ta kama ya zama Gaza.

An raba Kudus tsakanin sojojin Isra’ila a Yamma da na Jordan a Gabas.

Mamayar 1967

Kuma kasancewar an kawo karshen yakin ba tare da wata cikakkiyar yarjejeniya ba, an ci gaba da yaki daga lokaci zuwa lokaci inda kowane bangare ke dora wa dan uwansa laifi a shekarun da suka biyo baya.

A 1967 an sake gwabza wani yakin, inda Yahudawan Isra’ila suka mamaye Gabashin Isra’ila da Gabar Yammacin Kogin Jordan da yawancin Tuddan Golan hadi da Gaza da kuma Tsibirin Sina’u na Masar.

Akasarin ’yan gudun hijirar Falasdinu sun zauna a Gaza da Gabar Yamma da kuma kasashen Jordan da Siriya da Lebanon.

Tun daga lokacin Isra’ila ta hana wadannan Falasdinawa ko ’ya’yansu komawa su zauna a yankunansu na asali.

Ta tsaya kai-da-fata cewa Falasdinawan za su mamaye kasar, wanda hakan zai zama barazana ga kasar ta Yahudu.

Isra’ila ta ci gaba da mamaye Gabar Yamma, amma ta fice daga Gaza, sai dai har yanzu Majalisar Dinkin Duniya na daukar wannan yankin a matsayin wanda Isra’ila ta mamaye.

Isra’ila ta mayar da birnin Kudus hedikwatar Yahudu

Daga baya Isra’ila ta rika ikirarin cewa Birnin Kudus shi ne babban birninta inda Falasdinawa suka ce Gabashin Birnin zai kasance babban birnin kasarsu idan aka kafa ta.

Amurka ce kasar da ta fara amincewa da Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

A cikin shekara 50 da suka gabata Isra’ila ta gina gidajen Yahudawa a yankunan da ta mamaye inda a yanzu Yahudawa sama da 60,000 suke zaune a cikinsu.

Falasdinawa suna ganin hakan ya keta dokokin duniya kuma tarnaki ne ga zaman lafiyar da ake nema a tsakanin bangarorin biyu.

Kafuwar kungiyar Hamas

Kafuwar Hamas Sakamakon mamayar ta Yahudawan ce aka samu kafuwar Kungiyar Hamas mai reshen da yake gwagwarmaya da makamai da ake kira da Al-Kassam Brigade.

Isra’ila da Amurka da Tarayyar Turai da Birtaniya da wasu manyan kasashe sun ayyana ta a matsayin kungiyar ’yan ta’adda.

Hamas tana samun goyon bayan kasar Iran, wadda ake zargi da ba kungiyar tallafin makamai da horarwa.

Kuma Hamas din ce ke mulki a Zirin Gaza, inda a ranar Asabar da ta gabata ta ce ta kaddamar da hare-hare a kan Isra’ila ce saboda “ci gaba da zaluncin” da Isra’ila ke yi a kan Falasdinawa.

Kungiyar ta kafa hujja da hare-haren Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna a kauyukan Falasdinawa da makwabtanta da kai hari a wuraren ibada musamman Masallacin Kudus Mai Alfarma da kuma kisan dimbin Falasdinawa a bana.

Kunci da tsoro

Zirin Gaza mai tsawon kilomita 41 da fadin kilomita 10 yana tsakanin Isra’ila da Masar da kuma tekun Bahar Rum (Maliya).

An raba Zirin Gaza da sauran sassan duniya na tsawon shekara 17.

Hamas ce take mulkinsa tun shekarar 2007, sannan kasashen Masar da Isra’ila suna matukar takura wa mazaunansa.

Zirin mai mutum miliyan 2.3, na ɗaya daga cikin yankuna mafiya cinkoson jama’a a duniya.

Kasar Isra’ila ce take iko da sararin samaniyar Gaza da gabar tekunsa kuma takan takaita kayayyakin da za a ba da izinin shiga ko fita da su ta mashigin iyakar zirin.

Sai kuma Masar ke da iko kan masu shiga da fita ta iyakarta da Gaza.

Wannan ya sa Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya (HURIWA) ta bayyana Gaza da “Kurkukun fili mafi girma a duniya.”

Mazauna Gaza suna rayuwa cikin kunci da tsoro tare da daukar hare-haren Isra’ila a yankin a matsayin wadanda suka mayar da yankin baya.

Wannan ya sa aka rika fada daga lokaci zuwa lokaci a tsakanin Isra’ila da kungiyoyin Falasdinu a Gaza ciki har da Hamas da Islamic Jihad.

An ci gaba da zaman ɗar-ɗar a tsakanin Isra’ila da Hamas, sai dai harin da mayakan Hamas suka kai a ranar Asabar da ta gabata, ya zo ne ba tare da gargadi ba.

Sabon rikicin Hamas d Isra’ila

Hamas ta harba dubban makaman roka a kan Isra’ila, yayin da mayaƙa da dama suka kutsa kai a cikin iyakarta, suka mamaye yankunan Isra’ila, inda ake zargin sun kashe fararen hula da dama tare da kama wasu ciki har da sojojin Yahudu.

Nan take Isra’ila ta kai hare-hare ta sama, tana cewa tana auna “wuraren da ’yan ta’addan Gaza” suke ne.

Dalilin harin Hamas

Kafar labarai ta CNN a ranar Litinin ta bayyana dalilan Hamas na kaddamar da harin da kungiyar ta sa wa suna Harin Ambaliyar Al-Aksa.

Shugaban sashin soji na Hamas, Mohammed Deif, ya ce harin mayar da martani ne kan shafe shekara 16 da Isra’ila ta yi tana toshe hanyoyin rayuwa ga Gaza da harin da Isra’ila ta rika kai wa biranen da suke Yammacin Kogin Jordan a bara da tashin hankalin da ta haifar a Al-Aksa da karuwar kai harin da Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna suke yi a kan Falasdinawa da kara gina matsugunan Yahudawa a yankunan Falasdinawa.

Harin shi ne mafi muni tun lokacin da Isra’ila da Hamas suka gwabza yakin kwana 11 a shekarar 2021.

Hamas ta ce ta harba rokoki 5,000 zuwa cikin Isra’ila, ita kuma Isra’ilar ta tabbatar da cewa mayakan Hamas sun shiga cikin kasarta.

Rokokin da Hamas ta harba sun isa Arewa mai nisa har zuwa Tel Abib, sannan Hamas ta tura sojojinta cikin Kudancin Isra’ila.

Martanin Isra’ila

Sojojin Isra’ila sun mayar da martani ta hanyar kaddamar da harin da suka sanya wa suna Harin Takobin Karfe, a kan Kungiyar Hamas a Zirin Gaza, inda ta ayyana cewa “ta shiga yaki.”

Firayi Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya shaida wa al’ummarsa cewa “za a shiga wani yaƙi mai wahala da za a daɗe ana yi.”

A wata tattaunawa da shugabannin tsaro na gwamnatinsa, Benjamin Netanyahu ya ce: “Burinmu na farko shi ne mu kawar da dakarun maƙiya da suka kutso cikin ƙasarmu sannan mu dawo da tsaro da lumana a yankunan da aka kai wa farmaki.

“Burinmu na biyu a lokaci guda shi ne mu gallaza wa maƙiya a Zirin Gaza.

“Buri na uku shi ne mu ƙara toshe sauran ƙofofi ta yadda babu wani daban da zai yi kuskuren tsoma kansa a cikin wannan yaƙi.”

Ya ce, “Masoya mutanen Isra’ila. Mayakan Hamas sun mamayi kasar Isra’ila a safiyar yau a rana mai tsarki ta hutu ta Asabar, kuma sun kashe fararen hula da yara da tsofaffi haka siddan.

“Hamas ta farar da mugun yaki. Za mu yi nasara a wannan yaki, amma yana da matukar tsada.

“Wannan babbar rana ce mai wuya ga dukkanmu.”

An shammaci Isra’ila —Netanyahu

Isra’ila ta amince cewa an shammace ta wajen kai harin wanda ya zo a ranar da Yahudawa suka fi girmamawa.

Kuma mayakan Hamas suka kutsa cikin garuruwan Isra’ila suka kashe Yahudawa 1,400 tare da kame wasu da dama.

Sai dai ita ma Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 2,750 tare da raunata akalla 3,000 a harin da ta kai a Gaza.

“Wannan shi ne harin 9/11,” in ji Kakakin Sojin Isra’ila, Manjo Nir Dinar, “Sun cim mana. Sun ba mu mamaki, sun zo cikin sauri ta kusurwoyi da dama – ta sama da kasa da teku.”

Wakilin Hamas a kasar Lebanon Osama Hamdan ya shaida wa Reuters cewa harin ya nuna Falasdinawa za su iya cim ma manufofinsu “duk da karfin sojin Isra’ila da kwarewarsu.”

Manyan abubuwan da suka faru a lokaci da bayan harin:

Yadda sojin Hamas suka kutsa Isra’ila:

Wani bidiyo da birged din sojin Izz ad-Din al-Kassam ta tura ta telegram ya nuna sojin Hamas bakwai sun farmaki shingen tsallakawa zuwa Isra’ila na Erez daga Gaza a ranar Asabar.

Shammatar hukumomin leken asiri Jami’an Amurka a Erez daga Gaza a ranar Asabar.

Jami’an Amurka ma sun ce ba su samu wani gargadi ba ta hannun hukumomin leken asiri ba kan Hamas tana shirin kai hari a Isra’ila, wanda hakan ya sa Isra’ila ta gaza gano alamun kai mata harin rokoki.

Sannan kai hari a garuruwan Isra’ila da Hamas ta yi, ya sanya shakku kan fasahar bayar da bayanan sirri da Amurka ke yi ga Isra’ila, kamar yadda wani babban jami’in leken asiri na Amurka ya shaida wa CNN.

Kafa dokar ta-baci a Isra’ila

Isra’ila ta kafa dokar ta-baci inda ta bayar da sanarwar rufe dukkan makarantun kasar a ranar Lahadin da ta gabata.

Fara kai hari a Gaza

Isra’ila ta kai hari ta sama inda ta ruguza wani gida mai hawa 14 a Gaza.

Kuma Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinawa ta ce Isra’ila ta kai hari sansanin ’yan gudun hijira na Al-Shati da Jabalia, kuma gomman mutane sun mutu wasu sun jikkata.

Isra’ila ta datse Gaza gaba ɗaya

Ministan Tsaron Isra’ila Yoab Gallant ya yi umarnin a “Yi wa Zirin Gaza ƙawanya, babu shigar abinci, babu wuta sannan ba man fetur.”

Bakin da aka kashe a Isra’ila

Gwamnatin Amurka ta tabbatar da kashe Amurkawa 9 a harin da aka kai Isra’ila, kamar yadda Fadar White House ta bayyana.

Kuma an kashe mutanen kasar Thailand 12 tare da yin garkuwa da 11 kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Thailand ta tabbatar.

An raba mutum 123,000 da muhallansu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum dubu 123 da 538 aka raba da gidajensu a Gaza, akasari “saboda fargaba da damuwa a kan tsaron rayuwa da ruguza musu gidaje.”

Ofishin Babban Jami’in Ayyukan Jin kai na majalisar ya ce mutum 73,000 sun koma makarantu don samun mafaka.

Sauke bayanan Khamenei daga shafin X

Elon Musk, mai Shafin X (Twitter) ya sauke bayanan Shugaban Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei na yin murna da hare-haren Hamas a kan Isra’ila daga kafar.

Kuma ya ce kalaman Khamenei sun nuna karara Iran na da burin shafe Isra’ila daga bayan kasa.

Ƙasashe na rige-rigen kwashe mutanensu

Kasashen duniya sun yi ta rige-rigen kwashe mutanensu daga Isra’ila da Gaza, yayin da wasu kasashen ciki har da Najeriya suka dakatar da jigilar masu zuwa ziyarar ibada a Isra’ila.

Kasashen da suka fara kwashe mutanensu sun hada da Sabiya da Romaniya da Kazakhstan da Poland.

Amurka za ta taimaki Isra’ila da jiragen yaki

Kafar labarai ta Reuters ta ruwaito Sakataren Tsaro na Amurka, Lloyd Austin yana cewa Amurka za ta tura karin jiragen ruwa da na sama na yaki don nuna goyon baya da karfafa Isra’ila.

AU, Najeriya , China, Saudiyya, Masar da sauransu sun nemi a tsagaita wuta

Ministan Harkokin Wajen Najeriya  Ambasada Yusuf Tuggar da Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat sun bukaci bangarorin biyu su tsagaita wuta tare da komawa kan teburin tattaunawa don ceto rayukan fararen hula da kuma samar da kasashe biyu da za su zauna lafiya da juna.

Haka Masar da Saudiyya da Jordan sun bukaci a yayyafa ruwa ga wutar rikicin da ya taso s tsakanin kasashen Isra’ila da Falasdinu.