✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin matar aure da satar mazakuta a Abuja

Saura kiris a yi wa wata matar aure kisan gilla kan zargin ta da sace mazakutar wani mutum a Abuja.

Wata matar aure ta bayyana yadda jama’a suka kusa yi mata kisan gilla saboda zargin ta da sace mazakutar wani mutum a yankin Gosa da ke hanyar filin jiragen sama da ke Abuja.

Matar ta ce Allah na Ya kiyaye, domin saura kiris a aika ta lahira kan zargin, kamar yadda ta bayyana a lokacin da kwamishinan karbar korafi na Hukumar Birnin Tarayya, Ezekiel Musa Dalhatu.

Kwamishinan ya ziyarce ta ne domin ji daga gare ta, bayan zargin da aka yi mata na satar mazakutar ta tayar da kura.

Madam Rahab Emmanuel, mai shekaru 37 ta shaida masa cewa an yi mata kazafin satar mazakutar ne a lokacin da take hanyar zuwa gidan wasu da suka kira ta domin ta yi wa ’ya’yansu wankau.

Matar mai ’ya’ya hudu ta ce a hanya ne ta iske wani mutum a gaban wani shago inda ya ba ta N200 ta saya wa danta da ke tare da ita biskit.

Tana cikin neman gidan da aka kira ta wankau din ne mutum da ya ba ta N200 din ya yi ihu cewa mazakutarsa ta daina aiki.

Da jin haka ne wasu matasa suka yi dandazo suka fara lakada mata duka, suka kai kara ofishin ’yan banga.

“A ofishin ’yan banga matasan suka rika duka na, bayan sun daure hannuwana. Na dauko wayata zan kira mijina inda sanar da shi halin da ake ciki, amma suka kwace wayar,” in ji Madam Rahab.

Ta ce wasu makwabtanta da suka gan ta a wurin ne suka kira mijin nata ya zo, sannan ya kai kara ofishin ’yan sanda.

Kwamishina ya ce an sanar da ofishin ’yan sanda da ke Rukunin Gidaje na Trademore, inda ya bukace su da su gaggauta bincike don yi wa matar adalci.

Ya kuma gargadi jama’a su guji daukar doka a hannunsu kan mutanen da ake zargi da satar mazakuta, domin akan yi wa wasu kazafi, kuma hakan na zama barazana ga rayuwarsu.