✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turkiyya ta mayar da shari’ar Jamal Kashoggi hannun Saudiyya

Turkiyya dai na ta kokarin gyara dangantakarta da Saudiyya

Wata kotun kasar Turkiyya ta yanke hukuncin dakatar da shari’ar da ake yi wa ’yan Saudiyya 26 bisa zargin kashe dan jaridar nan, Jamal Kashoggi, tare da mayar da shari’ar zuwa Saudiyya.

Mai kimanin shekara 59 a duniya, an kashe Jamal ne a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul, babban birnin Turkiyya a ranar biyu ga watan Oktoban 2018.

A makon da ya gabata, mai shigar da kara a kasar ta Turkiyya ya yi kira da a dauke shari’ar a mayar da ita hannun hukumomin Saudiyya.

Daga bisani dai Ministan Shari’a na Turkiyya ya ce za su amince da bukatar.

Daukar matakin dai na zuwa ne duk da gargadin da kungiyoyi masu rajin kare hakkin dan Adam ke yi cewa akwai fargabar yin rufa-rufa muddin aka mayar da shari’ar zuwa Saudiyya.

Wani rahoton sirri na gwamnatin Amurka a 2018 dai ya zargi Yariman Saudiyya, Muhammad Bin Salman, da hannu dumu-dumu a kisan na Kashoggi.

Sai dai budurwar Kashoggin, Hatice Cengiz, wacce ’yar asalin Turkiyya ce, ta ce za ta daukaka kara, inda ta ce kasarta na da tsarin shari’a mai share hawayen mutane, ba kamar Saudiyya da iyali daya ke jagoranta ba.

Turkiyya dai na ta kokarin gyara dangantakarta da Saudiyya da ma sauran kasashen yankin.

A watan Nuwamban 2018, Shugaban Turkiyyar, Recep Tayyip Erdogan, ya zargi hukumomin Saudiyya da cewa su ne suka shirya kisan.

Sai dai tuni hukumomin na Turkiyya suka yi mi’ara koma baya daga matsayin nasu, inda suka yi kira da a gudanar da binciken kasa da kasa a kan lamarin.