✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta sanya wa masu Umarah wa’adin ficewa daga ƙasar

Saudiyya ta ce duk wanda ya wuce lokacin ko shakka babu ya saɓa ka’ida sannan kuma zai fuskanci hukunci.

Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe da duk wani baƙo da ke ƙasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar.

Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta ɗauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa.

Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga ƙasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita.

Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a ƙasar har ya wuce lokacin da keɓe, to ko shakka babu ya saɓa ka’ida sannan kuma zai fuskanci hukunci.

Mahukuntan sun buƙaci mutane da ma kamfanonin da ke shirya zuwa aikin Umrah da su kiyaye da waɗannan lokuta da aka ƙayyade.

An kuma yi gargaɗin cewa duk wani jinkiri na barin mutane, ƙasar za a ɗauke shi kamar karya doka.

Ta ce duk kamfanin da aka samu da ƙin bayyana mutanen da suka ƙi koma wa ƙasashensu to za a ci tararsu riyal dubu 100.