Assalamu Alaykum; ina maku marhabin da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da zasu zo cikinsa, amin. Ga tunawarwa musamman ga ma’aurata kan yadda zasu rayas da zaki da dadin cikin Ramadan a sauran kwanaki masu zuwa har wani Ramadan din Ya kara tsagayowa. Da fatan Allah Yasa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar dasu, amin.
Ramadan, Watan Alheri!
Alheran da watan ramadan yake saukarwa cikin al’umma basu da iyaka, kuma ni’imomin da bayin Allah duka ke moruwa dasu a cikinsa basu misaltuwa. Mafi muhimmanci daga cikin su shine yadda ya kan sa gaba daya al’umma ta maida hankali ga bautar Allah da dagewa wajen yin ayyukan ibada don neman kusanci ga Allah SWT wadanda kafin ramadan din ba a yinsu. Haka kuma Ramadan ya hada kungiyoyi da yawa na alheri, wadanda ke kokarin yin ayyukan sadaukarwa da taimakon mabukata; da yawan almjirai kan mance da yunwa ko su nemi aminci su rasa. Ga kungiyoyin ciyar da mabukata da raba abinci a masallatai da wuraren taruwar mutane. Da sauran ire-iren kyautuka, sadaka da ayyukan sadaukarwa da suke yalwata cikin al’umma duk a dalilin zuwan watan alfarma na Ramadan. Sai dai abin takaicin shine da yawa daga cikin wadannnan kyawawan ayyuka su kan tsaya cak bayan Ramadan har sai wani Ramadan din kuma ya kara tsagayowa.
Tunatarwa garemu duka shi ne mu sani cewa in dai domin Allah muke yin duk wadannan kyawawan ayyuka a cikin Ramadan, to mu sani fa cewa Allah na nan a dukkan watannin nan goma sha biyu na shekara ba wai lallai sai cikin Ramadan kadai ba! Don haka ba daidai ba ne a ce daga cikin wata goma sha biyun shekara, cikin wata daya ne kadai muke dagewa da kara neman kusanci ga Allah Madaukakin Sarki, cikin wata daya ne kadai muke kokarin karanta Littafin Sa mai tsarki. Musamman in aka yi la’akari akan yadda da yawanmu ke dagewa wajen wasu karance-karancen don samun nasarar rayuwar duniya amma kuma a kasa dagewa wajen karantawa da fahimtar ma’anonin Littafi daya don samun nasarar ranar gobe kiyama, duk kuwa da irin dadi da farinciki da kan cika zuciya bayan karatunsa. Don haka kar muyi sake mu bari shaidan yayi mana wayau ya hana mu karanta Littafin Madaukakin Sarki mu na bata lokaci wajen karanta wanda kaskantattun bayin sa suka rubuta.
Haka nan batun ciyarwa da sadaka ga marasa galihu; ba sai a cikin azumi ne kadai zamu runka wannan muhimmin aiki ba; mu sani ko bayan Ramadan akwai wadannan marasa galihun a cikin al’umma haka kuma bukatar su ta abinci da sauran kayan bukatu tana nan; in muka yi la’akari zamu ga cewa bukatun miskinai da almajirai tafi tsananta bayan Ramadan, domin cikin Ramadan suna azumi kamar kowa; bukatarsu ta abinci ba ta kai ta yanzu da ba a azumi ba. don haka bayan Ramadan ne mafi dacewar lokacin taimaka masu sama da cikinsa ma.
Mu tuna cewa Allah Yana tsananin son masu taimako da kyautatawa ga marasa galihu; in muna bin ma’anonin Al’kur’ani Mai Girma, za mu lura da yadda Allah ke yawan umartarmu a kan sadaka, da ciyarwa dominSa SWT, da kyautatawa ga mabukata da yi masu magana mai kyau; don haka kamar yadda aka kula da mabukata da talakawa cikin Ramadan, to bayan ramadan ma sai a cigaba da rayar da wannan kyakykyawan aikin.
Haka nan sauran ibadojin da muka yi sabo da su cikin ramadan, kamar su yin sallolin farilla cikin jam’i, yin sallolin tsayuwar dare, kyautata zamantakewa cikin iyali, kyautata zumunta da makwabta da ‘yan’uwa; karin kyautatawa wajen riko ga iyali, hakuri da kau da kai; da dai duk wani kyakykyawan aiki da mutum ya dabi’antu da shi cikin Ramadan, to sai yayi riko da shi riko mai karfi, kar ya yarda yayi sakaci har ya sullube mashi; mu tuna cewa watan Ramadan watane na musamman, domin watan albarkane, a kan daure manyan shaydanu a cikin tsawon kwankinsa gabadaya, don haka aikin alheri bai yin wahala cikin Ramadan. Amma yanzu kuwa wadannan shaydanu a sake suke kuma sun dawo daga hutun dolensu na wata daya da sabon tsari da kuma karin kuzari da karsashin aikin yadda zasu halakar da bil’adama; don haka dole sai an dage an yakesu da karfin gaske, ta hanyar yin kyakykyawan riko ga duk wani aikin alheri da aka faro cikin Ramadan, kuma har a samu tsiro da wani sabon aikin alherin cikin yardar Allah SWT. Da fatan Allah Ya taimakemu duka Ya bamu iko mu ci karfin dukkan shaydanu, Ya kuma tsaremu daga dukkan sharrinsu, amin.
Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.